Dora ashararai kan shugabanci yana daga cikin alamomin tashin Alkiyama
Daga Imam Murtada Muhammad Gusau (Abu Mus’ab)Masallacin Nagazi, Okene, Jihar Kogi Huduba ta Farko:Lallai dukkan godiya ta tabbata ga Allah da Ya shiryar da mu ga Musulunci, ba mu kasance masu shiryuwa ba, ba domin ya shiryar da mu ba. Kuma ina shaidawa ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya […]
Daga Imam Murtada Muhammad Gusau (Abu Mus’ab)
Masallacin Nagazi, Okene, Jihar Kogi
Huduba ta Farko:
Lallai dukkan godiya ta tabbata ga Allah da Ya shiryar da mu ga Musulunci, ba mu kasance masu shiryuwa ba, ba domin ya shiryar da mu ba. Kuma ina shaidawa ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya. Yana hukunta abin da Ya so kuma yana aikata abin da Ya yi nufi. Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu Annabi Muhammadu (SAW), bawanSa ne kuma ManzonSa ne; ya isar da manzanci kuma ya rike amanar da Allah Ya dora masa da gaskiya, kuma ya yi nasiha ga al’umma. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa da duk wanda ya bi su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Lallai ina yi muku wasiyya da ni kaina da jin tsoron Allah (SWT), domin babu tsira a nan duniya da kuma Lahira, sai da tsoron Allah, kuma shi ne tushen dukkan alheri.
Ya ku Musulmi! Lallai mu sani, gyaruwar al’umma ta ta’allaka ne a kan gyaruwar shugabanni, kuma lalacewar al’umma ta ta’allaka ne a kan lalacewar shugabanni. Abin nufi a nan shi ne; a duk lokacin da shugabanni suka zamo na kirki, to ana sa ran mabiya su zamo na kirki, haka duk lokacin da shugabanni suka zama na banza, to, lallai mabiya ma haka za su kasance. Shi ya sa Musulunci ya bada muhimmanci sosai a kan cewa lallai jama’a su yi kokarin ganin wadanda za su jagorance su mutanen kirki ne ba ashararai ba, adilai ne ba azzalumai ba, yin haka zai sa zaman lafiya da ci gaba su yawaita a kasa.
Ya ku Musulmi! Hakika Annabi (SAW) ya bada labari cewa; yana daga alamomin tashin Alkiyama, ya kasance ana shugabantar da ashararar mutane, ko mutanen banza jahilai, wadanda ba sa neman shiriya da Littafin Allah da kuma Sunnar ManzonSa (SAW), sannan kuma ba sa jin nasiha, kuma ba sa wa’azantuwa a kan al’umma.
Imamu Ahmad da Al-Bazzar sun ruwaito Hadisi daga Jabir dan Abdullahi (RA) ya ce: “Lallai Annabi (SAW) wata rana ya ce da Ka’ab bin Ujrata (RA) “Allah Ya tsare ka ya kai Ka’ab daga shugabancin mutanen banza, jahilai wawaye.” Sai Ka’ab ya ce; Mene ne shugabancin mutanen banza wawaye ya Manzon Allah?” Sai Annabi ya ce; “Wasu shugabanni ne da za su zo nan gaba bayan na wuce, ba sa bin shiriyata, kuma ba sa bin tafarkina. Saboda haka duk wanda ya gaskata su a kan karyarsu, kuma ya taimake su a kan zaluncinsu, to, ba ya tare da ni, kuma ba na tare da shi, kuma ba zai taba shan ruwan Tafkina ba. Kuma duk wanda bai gaskata su a kan karyarsu ba, kuma bai taimake su a kan zaluncinsu ba, to, wadannan suna tare da ni, kuma ina tare da su, kuma za su sha ruwan Tafkina.” Annabi (SAW) ya ci ga ba da cewa; “Ya kai Ka’ab bin Ujrata! Ka sani Azumi garkuwa ne, kuma sadaka tana kau da zunubi, Sallah neman kusanci ne zuwa ga Allah, ko kuma hujja ce. Ya Ka’ab bin Ujrata; ka sani duk wata tsoka da ta ginu da haram, to, har abada ba za ta shiga Aljanna ba, wuta ita tafi cancanta da ita. Ya Ka’ab bin Ujrata; a kullum mutane suna yin sammako, akwai wanda zai sayar da rayuwarsa, akwai wanda zai ’yanto ta, ko ya halakar da ita.” Ahmad da Bazzar ne suka ruwaito.Ya ku mutane! Mutumin banza, jahili, shi ne mai karancin hakali, mai karancin tunani, mara hangen nesa, wanda ko kansa ba zai iya shugabanta ba, balle ya shugabanci waninsa.
A wani Hadisin Annabi (SAW) ya ce: “Alkiyama ba za ta tsaya ba, har sai ya kasance manufakan cikin al’umma su ne za su yi shugabanci.” dabarani ya ruwaito shi. Munafukai za ka same su masu karancin imani, masu karancin tsoron Allah, makaryata, jahilai, azzalumai, mayaudara, kansu kawai suka sani.
Ya ku bayin Allah masu girma! Lallai idan aka wayi gari masu mulkin mutane ko shugabanninsu ka jagororinsu, suka kasance ashararai, mutanen banza, jahilai, wawaye, to, lallai al’amarinsu zai lalace! Sai a wayi gari, ana girmama mutanen banza a gwamnati, ana wulakanta mutanen kirki, a yarda da mayaudara, a wulakanta masu amana. Sai ya kasance jahilai su ne masu fada-a ji a gwamnati, masana kuma ba su da bakin magana, domin ko sun yi magana, ba ta da tasiri a wurin gwamnati.
Babban Malami Imamush-Sha’abiy (Allah Ya jikansa da rahama) ya ce: “Alkiyama ba za ta tsaya ba, har sai an wayi gari ilimi ya koma ana kallonsa jahilci, jahilci kuma ana kallon shi ne ilimi.” Wannan kuwa duk zai faru ne a cikin wannan zamani da al’amura suka birkice, suka lalace suka rincabbe, aka rasa shugabanni nagari. Kuma Annabi (SAW) ya fada a Hadisin Abdullahi dan Umar (RA) cewa: “Lallai yana daga alamomin Alkiyama; za a dankwafar da mutanen kirki, kuma a daukaka mutanen banza, ashararai.” Al-Hakim ya fitar a Al-Mustadrak.
Ya ku Musulmi!A yau duk wanda yake raye ya tabbatar kuma shi shaida ne cewa lallai duk abin da Annabi (SAW) ya fada ne ke faruwa. Domin an wayi gari mafi yawan wadanda ke shugabantarmu ashararai ne, sai fa ’yan kadan daga cikinsu, domin duk yadda al’amari ya kasance ba a taruwa a zama daya, kuma ba a rasa na kirki a kodayaushe.
Don haka wajibi ne a gare mu kowa ya yi kokari ya ga cewa ya ba da gudunmawa gwargwadon ikonsa, domin ya zama wadanda za su shugabance mu, mutanen kirki ne. Lokacin yin shiru ya wuce, ba zai yiwu ba a ce mutanen banza ke ta jagorantarmu.
Allah Ya albarkace ni da ku a cikin bin Alkur’ani da Sunnah, kuma Ya amfanar da ni da ku da abin da ke cikinsu na ayoyi da hikima, ina fadin abin da kuke ji, ina mai neman gafarar Allah gare ni da ku da sauran Musulmi daga dukkan zunubi da kuskure. Ku nemi gafararSa, lallai ne Shi Mai gafara ne Mai jin kai.
Huduba ta Biyu:
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, ina gode maSa godiya mai yawa, ina neman taimakonSa, ina neman gafararSa, kuma ina tuba zuwa ga re Shi. Kuma ina shaidawa, lallai babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake, ba Ya da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu Annabi Muhammad (SAW) bawanSa ne, kuma ManzonSa ne, ya bar mu a kan hanya mai haske, fara tas, darenta kamar yininta yake, ba wanda zai karkace daga gare ta, sai halakakke. Allah Ya kara tsira da aminci a gare shi da iyalansa da sahabbansa da dukkan mabiyansu da kyautawa har zuwa Ranar karshe.
Bayan haka, ya ku Musulmi! Lallai dukkanmu Allah zai kama mu da laifin rashin tabuka komai, a kan samar wa al’umma nagartattun shugabanni. A yau dai dukkaninmu masu shaida ne a kan irin halin da kasarmu mai albarka da yankinmu mai albarka na Arewa suka shiga, sakamakon rashin shugabanci nagari. To abin da ya faru ya riga ya faru, yanzu abin tambaya shi ne; me muke yi domin kokarin samar da shugabanni na kwarai? Ko har yanzu barci muke yi ba mu farka ba?
Ya ku bayin Allah! Mu sani, lallai asalin shugabanci ko jagoranci, shi ne a shugabantar da wanda ake ganin ya dara kowa ilimi da adalci da gaskiya da amana da lafiya da rashin nuna bambanci a tsakanin ’jama’a da rashin son kai da sauransu. To, amma a yau abin ba haka yake ba, fasikai da mutanen banza da ashararai da mayaudara da mashaya da mazinata da barayi ne ke shugabantarmu. Saboda suna da kudi, ko don dangartakarsu, ko wani matsayi da suke da shi, ko saboda tsabagen rashin kunyarsu, ko don su ’ya’yan manya ne, amma ba domin cancanta ko dacewa ba. Duk wannan saboda lalacewar al’amura ko kuma mutanen kirki sun yi saranda sun mika wuya, sun yarda mutanen banza sun ci su da yaki.