dorewar sabon titin jirgin kasa

Ranar Talata, 26 ga Yulin 2016, Shugaba  Muhammadu Buhari ya kaddamar da hada-hadar sufurin jirgin kasa a kan managarcin tsarin titin dogo a Najeriya. Titin jirgin kasan mai nisan kilomita 186.5 ya samo asali ne tun zamanin mulkin Olusegun Obasanjo, sannan aka himmatu wajen aiwatar da shi a zamanin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan, an kuma […]

dorewar sabon titin jirgin kasa
dorewar sabon titin jirgin kasa

Ranar Talata, 26 ga Yulin 2016, Shugaba  Muhammadu Buhari ya kaddamar da hada-hadar sufurin jirgin kasa a kan managarcin tsarin titin dogo a Najeriya. Titin jirgin kasan mai nisan kilomita 186.5 ya samo asali ne tun zamanin mulkin Olusegun Obasanjo, sannan aka himmatu wajen aiwatar da shi a zamanin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan, an kuma gina shi a kan kudi Dala biliyan guda da miliyan 460. Aikin ya samu wani kason kudin Dala miliyan 500 na fara aiki daga bankin Edim na kasar Sin.
A lokacin kaddamarwa, Buhari ya ce:” Hada-hadar sufurin jirgin kasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna zai yi matukar inganta harkokin sufuri tsakanin babban birnin tarayya da Jihar Kaduna, a wani sashe da ake da dimbin albarkatun kafa masana’antu da ayyukan gona, ga kuma dimbin ma’aikata da ke karuwa.
Shugaban kasar ya tuna baya da cewa: Sanannen al’amari ne a tsakanin shekarar 1963 zuwa shekarun 1980, Najeriya na da managarcin titin hada-hadar sufurin jirgin kasa da ke dakon kayan amfanin gona da dabbobi da ma’adanai zuwa tashoshin jiragen ruwan Legas da Fatakwal, inda daga wurin ake fitar da su zuwa wasu sassan duniya. Don haka muke hange da fatan ganin dawowar tsarin da aka ji dadinsa a baya, ta yadda zai kara bunkasa, tare da dawo da martabar sufurin jiragen kasa da bikin yau ke nuni a kansa.”
Duk da cewa aikin sufurin jirgin kasa a tsakanin Abuja zuwa Kaduna an bijiro da shi ne cikin shekarar 2009, sai dai aikin bai kankama ba, sai shekarar 2011, inda aka yanke matsayar kare shi a shekarar 2014. Rashin kammala aikin da wuri an danganta shi ne da kin bayar da kason kudin gwamnatin tarayya a kan kari. Kuma kammala aikin da aka yi cikin shekara guda da hawan wannan gwamnati, alama ce da ke nuni da jajircewar Buhari wajen farfado da sufurin jirgin kasa.
Sai dai mun yi zaton za a yaba wa tsohon Shugaban kasa Jonathan, musamman a lokacin bikin kaddamarwa ko don kawar da sukar adawa da ke tsakanin Jam’iyyun PDP da APC, kan ko wa ya cancanta a yaba masa game da aiwatar da wannan managarcin aiki, mai alfanu.
Sannan farfado da sufurin jirgin kasa kadai ba zai isa ba. dorewar tsarin shi ne mafi alfanu. Shugaban kasa ya bayyana cewa bikin makon jiya share fagen shirin bunkasa sufurin jirgin kasa ne na shekara 25. Don haka akwai bukatar ganin labarin ya sauya, ta yadda za a samar da tsarin zamani a titin jirgin kasa.
Sanannen al’amari ne cewa, tun daga shekarar 1964, Hukumar sufurin Jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ke aiwatar da ayyukanta bisa doron gibin kasafin kudi. Akwai bukatar isassun kudi daga gwamnati da zai tallafeta.  Sakaci da lalacin ma’aikatan gwamnati suka yi rugu-rugu da hukumar. Muna kira ga gwamnati ta sake fasalin tafiyar da wannan fanni a matsayin hada-hadar kasuwanci. Dole a samu hukumar gudanarwa tsayayya da za ta tabbatar da nagarta mafi inganci wajen a hada-hadr sufurin. A fito da tsarin gyara da zai tabbatar da dorewar layukan titin ba tare da wani nakasu ba.
Muna kira ga gwamnati ta sanya ido kan daukacin kwangilolin da Hukumar Jiragen kasan Najeriya ta NRC za ta bayar, saboda a mummunan tsari a kan bayar da kwangilolin bogi, ta yadda kudin shigar hukumar za su salwanta. Kaso mafi tsoka na wadannan kudi sukan taru ne a lalitar shugabannin da aka dora wa alhakin kula da sufurin jiragen kasa. Sai a yi ta aiwatar da ayyukan zamba cikin aminci, da suka hada da bayar da jabun tikiti ga fasinjoji da miyagun ayyukan da aka yi ta tafkawa a baya.
A karkashin sabon tsari, muna bai wa Hukumar NRC kwarin gwiwar horar da ’yan kasa da ke aikin kere-kere don a tafi da su wajen aiwatar da gyare-gyaren titin jirgin kasa. Al’amarin zai yi matukar muni idan har gwamnati ta danka harkar gyaran sabon titin jiragen kasa ga mutanen Sin, wadanda a nan gaba za su bar shirin su yi gaba. Idan har ba a horar da masu kere-kere ’yan Najeriya ba, da za su ci gaba da tafiyar da aikin, shirin na iya durkushewa da zarar ’yan kasar Sin sun fice. A shigo da injiniyoyin Najeriya cikin harkar fadadawa da zamanantar da shi tare da tabbatar da dorewar shirin.
Kuma muna kira ga gwamnati ta yi hanzari wajen gyara fasalin masana’antar karafa ta Ajaokuta da ke Jihar Kogi don samar da isassun karafan gyaran titunan jiragen kasa. Yin hakan zai hana kashe dimbin kudin musayar kasashen waje don shigo da kayan gyara. Farfado da masana’antar karafa ta Ajaokuta zai samar da aikin yi ga dimbin matasa a kasar nan.
kaddamar da hada-hara sufurin jirgin kasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna ya bude sabon babi a Najeriya. Sai dai dole a tabbatar da dorewarsa.