Doug Jones ya buge dan takarar da Shugaba Trump ke so

Dan jam’iyyar Democrat, Doug Jones ya buge dan takarar da Shugaban Amurka Donald Trump ke goyon baya a zaben Majalisar Dattawa na Jihar Alabama. Wannan nasarar ta sa Doug Jones ya zama dan jam’iyyar Democrat na farko a cikin shekara 25 da ya samu nasarar lashe zaben kujerar Majalisar Dattawa daga Jihar Alabama, bayan da […]

Doug Jones ya buge dan takarar da Shugaba Trump ke so

Dan jam’iyyar Democrat, Doug Jones ya buge dan takarar da Shugaban Amurka Donald Trump ke goyon baya a zaben Majalisar Dattawa na Jihar Alabama.

Wannan nasarar ta sa Doug Jones ya zama dan jam’iyyar Democrat na farko a cikin shekara 25 da ya samu nasarar lashe zaben kujerar Majalisar Dattawa daga Jihar Alabama, bayan da ya tsaya takarar neman zaben kujerar tare da dan jam’iyyar Republican Roy Moore kamar yadda BBC ta ruwaito.

BBC ta ruwaito cewa nasarar Mista Jones ta bayar da mamaki kuma ta jaddada rashin amincewar Amurkawa da akidar Shugaba Donald Trump, domin ya nuna tsananin goyon bayansa karara ga Mista Moore. duk kuwa da cewa wasu jiga-jigan jam’iyyarsu sun ki bayar da na su goyon bayan.

A lokacin gangamin neman zaben, an yi zargin Mista Moore da cin zarafin wasu ‘yanmata, amma ya fito ya karyata zargin.

Jihar Alabama za ta samu wakilcin Demokrat a Majalisar Dattawan Amurka, wanda hakan zai iya bai wa ‘yan Demokrat dama wajen mamaye majalisar a zaben rabin zango wanda zai wakana badi.

Shugaba Trump ya taya Mista Jones murna a shafinsa na twitter bayan kafofin sadarwar Amurkar sun bayyana shi a matsayin wanda ya samu nasarar zaben.