DPO ya biya wa saurayi sadakin aure

Amarya Maryam Isa ta nuna farin cikinta kan taimakon da DPO Lawan ya yi.

DPO ya biya wa saurayi sadakin aure

DPO Lawan Abdullahi da Sakataren Fadar Sarkin Danbushiya, Umaru Yakubu

Baturen ’Yan sanda (DPO) na ofishin ’yan sanda da ke Danbushiya a Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna Lawal Abdullahi ya taimaka wa wani matashi da kudin sadaki domin ya auri budurwarsa.

Matashin mai suna Aliyu Jibril yana soyayya da wata marainiya mai suna Maryam Isa, amma kuma ba shi da kudin da zai iya aurenta.

Bayan sun dauki lokaci suna soyayya sai dangin Maryam suka bukaci ya kai kudin gaisuwa Naira dubu 20, domin a fara tattauna batun aurensu, amma ya gaza.

Sakataren Sarkin Danbushiya Malam Umaru Yakubu ya ce, bayan dangin yarinya sun ga ba ya da alamar biyan wannan kudi sai suka bukaci ya rabu da ita domin wasu manema su fito.

“Duk matakin da ya kamata a bi don raba su an bi, amma abin ya faskara, sai suka kawo maganar zuwa fada.

“Muka kira bangaren yaro da bangaren yarinya da yaron da kuma yarinyar. Muka tambaye shi da me yake neman yarinyar ya ce da aure.

“Aka shaida masa idan da aure ne to ya fito ko a mika batun ga hukuma. Nan take aka fada masu su je, su kawo kudin gaisuwa Naira 20,000.

“Muka rabu da su a kan za su kawo kudin, amma har kusan mako biyu babu labari. Da muka auna sai muka ce da shi ya kyale yarinyar domin ba ya da karfin yin aure.

“Muka buga amma abu ya faskara. Daga nan sai sarki ya sake neman iyayen yarinyar da na yaron da yaran biyu aka sake zama.

“Sarki ya ce, an yi magana za ka kawo abin da za a yi wannan aure tunda yarinyar marainiya ce, amma kuma ba ka kawo komai ba.

“Da aka lura dai ba zai iya ba, sai aka mika batun ga ’yan sanda. Daga nan DPO ya tambayi iyayen ko sun yarda a daura aure suka ce eh, muddin ya biya sadaki. Aka yi lissafin kusan Naira 51,000, sai DPO ya ce ya biya sadakin.

“Nan take aka biya kudi Sarki ya nemi wakilan yarinya da na yaro a fadarsa, washegari aka daura aure a gaban limamai,” in ji shi.

Malam Umaru ya ce, daga nan ne aka cika da mamaki tare da yi wa DPO fatar alheri.

Yayar mahaifiyar amaryar, Hafsat Abdullahi ta ce, sun cika da mamaki lokacin da DPO ya biya sadakin domin a cewarta sun kai kara ce don a raba masoyan tunda saurayin ya kasa biyan kudin.

“Muna fata a ci gaba da samun irin wadannan mutanen kirki a cikin ’yan sanda domin gaskiya mun ji dadin abin da ya yi wa yarinyar,” in ji ta.

Amarya Maryam Isa ta nuna farin cikinta kan taimakon da DPO Lawan ya yi na biyan sadakin wanda hakan ya sa aka daura mata aure da mijinta.

Sarkin Danbushiya, Malam Muktar Haruna wanda shi ne ya daura auren a ranar 19 ga Yuli a fadarsa ya ce, zuwan DPO Lawan yankin nasu alheri ne domin ya taimaka wajen samar da tsaro a yankin.

Ya yaba wa Rundunar ’Yan sanda, musamman Kwamishina M.Y Garba bisa samar da motar sulke a ofishin ’yan sanda da ke unguwar da zuwan DPO Lawan wanda ake amfani da ita wajen samar da tsaro a yankin.

Wani mazaunin yankin Ibrahim Maiturare ya ce, mutanen yankin suna farin ciki da samun wannan dan sanda a yankin saboda abin alherin da yake yi.

Ya ce, ba ya karbar kudi da sunan beli domin yana nanata cewa beli kyauta ne kamar yadda Rundunar ’Yan sandan Kasa ta sha fadi.

Kokarin jin ta bakin DPO Lawan Abdullahi a kan lamarin ya ci tura, amma Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar DSP Mohammed Jalige ya bayyana DPO Lawan a matsayin jajirtacce da ke da kwarewa a aikin ’yan sanda.

Ya ce, suna jin dadin yadda yake tafiyar da aikinsa a yankin Sabuwar Kaduna, musamman a fannin tabbatar da kyakkyawar mu’amala a tsakanin mazauna yankin da ’yan sanda.

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano

Ɗan Gwamnan Jigawa ya rasu kwana guda bayan rasuwar mahaifiyarsa