DPP ta fitar da dan takarar Gwamna a Kano
Jam’iyyar DPP ta fitar da Barista Muhammad Tijjani, a matsayin dan takararta na Gwamnan Jihar Kano, a yayin wani zaman tattaunawa na masu ruwa da tsaki da kuma dattawan jam’iyyar da ya gundana, don fitar da gwaninsu a zaben 2015. A jawabin Shugaban Jam’iyyar ta DPP Alhaji Jibrin Muhammad Hassan, bayan bayyana Barista Tijjani a […]
Jam’iyyar DPP ta fitar da Barista Muhammad Tijjani, a matsayin dan takararta na Gwamnan Jihar Kano, a yayin wani zaman tattaunawa na masu ruwa da tsaki da kuma dattawan jam’iyyar da ya gundana, don fitar da gwaninsu a zaben 2015.
A jawabin Shugaban Jam’iyyar ta DPP Alhaji Jibrin Muhammad Hassan, bayan bayyana Barista Tijjani a matsayin dan takararta, ya bayyana cewa ’yan jam’iyyar sun cika da farin cikin komawar Barista Tijjani cikin jam’iyyarsu, daga tsohuwar jam’iyyarsa ta Lebo ta ’yan kwadago, domin a cewarsa, shi Barista mutum ne mai ilimin addini da na shari’a da kuma ilimin zamani.
Barista Tijjani dai ya kasance tun a can baya, dan jam’iyyar Lebo ne, kuma fitacce a cikinta, amma daga baya ya koma cikin jam’iyyar DPP, har kuma ya yi nasarar samun tsayar da shi dan takarar Gwamna a cikinta.
Da farko, ya bayyana shigar Barista Tijjani cikin jam’iyyar DPP da cewa alheri ne a gare shi, da kuma ita jam’iyyar. Haka nan ya ce barinsa jam’iyyarsa ta baya da cewa, ya bar ta ne a saboda rashin alkiblar shugabanci.
Ya kuma ce zai yi amfani da matsayin da aka ba shi, domin taimaka wa jama’a, tare da kira ga ’yan jam’iyyar da su ba shi cikakken hadin kai da goyon baya, wajen daukaka jam’iyyar zuwa madaukakin matsayi. Haka nan ya yi fatan Ubangiji Ya ba su nasara a kan abin da suka sanya a gaba.