DPR ta gano gidajen man fetur 50 na bogi a Akwa Ibom
Hukumar dake kula da sayar da man Fetur ta Najeriya DPR da ke da cibiyar ofishinta a garin Eket jihar Akwa Ibom. Ta ce, ta gano gidajen man fetur 50 na bogi a jihar. Kwantilrolan gudanarwa na DPR a jihar Mista Tamunoiminabo Kingsley-Sundaye, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a […]
Hukumar dake kula da sayar da man Fetur ta Najeriya DPR da ke da cibiyar ofishinta a garin Eket jihar Akwa Ibom. Ta ce, ta gano gidajen man fetur 50 na bogi a jihar.
Kwantilrolan gudanarwa na DPR a jihar Mista Tamunoiminabo Kingsley-Sundaye, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a garin Eket yau Litinin.
Ya bayyana cewa, wadannan gidajen man fetur din basu karbi lasisin fara gudanar da harkokin kasuwancin su daga Gwamnatin tarayya ba kuma basu bi tsarin gina gidajen man ba.