DPR ta kulle gidajen mai 6 a Gombe

Sashin kula da albarkatun man fetur ta kasa DPR a Jihar Gombe ta kulle gidajen mai guda shida saboda sayar da mai din a kan farashin Naira 210.   Hukumar ta rabu kashi uku ne don gudanar da aikin ta inda wasu suka je Gombe ta Arewa wasu Gombe ta Kudu wasu kuma Gombe ta […]

DPR ta kulle gidajen mai 6 a Gombe

Sashin kula da albarkatun man fetur ta kasa DPR a Jihar Gombe ta kulle gidajen mai guda shida saboda sayar da mai din a kan farashin Naira 210.
 
Hukumar ta rabu kashi uku ne don gudanar da aikin ta inda wasu suka je Gombe ta Arewa wasu Gombe ta Kudu wasu kuma Gombe ta tsakiya inda suka zaga gidajen mai don ganin yadda ake sayar da mai din.
 
A Gombe ta Kudu tawagar ta ziyarci garin Tumu da Kashere da Billiri da wasu gidajen mai da ke kan hanyar Yola zuwa Gombe inda a wannan bangaren suka kulle gidajen mai biyu daya a Tumu daya a Billiri mai suna Tukur Dahiru Muhammad.
 
Kwanturolan DPR din na Gombe Abdullahi Abawa, da yake Karin haske a garin Billiri ya bayyana cewa su na zaga gidajen mai din ne dan tabbatar  da ana sayar da mai din akan farashin naira 145 farashin gwamnati akan kowacce Lita.
 
Wani fasinja mai suna Hammadu Mohammad, da ya sha mai a wuni gidan mai mai suna Mubbis a garin Kashere kan farashin naira 210 ya koka wa DPR inda nan take kwanturolan na DPR ya sa aka mayar da lissafin kan naira 145 kuma aka mayar masa da sauran kudin sa wannan ya sa aka kulle gidan man. 
 
A Gombe ta tsakiya hukumar ta rufe gidaje mai uku sannan a Gombe ta arewa kuma ta rufe daya.
 
Da yake zantawa da manema labarai a ofishin sa Kwanturolan Abdullahi Abawa, ya ce jama’a sunyi murna na yadda suka sa ake sayar da mai din a wasu gidajen mai din da suke da mai a farashin gwamnati kan 145.
 
Abdullahi Abawa, ya bada da cewa ba gwamnati ne matsalar man fetur ba yan kasuwar man fetur din ke da matsala dan haka yake kira da suji tausayin al’umma su kawo mai din.
 
Wasu direbobi da muka zanta dasu a garin Billiri sun nuna jin dadin su kan yadda DPR ta tilastawa masu gidajen mai sayar musu da mai din a farashin gwamnati