DPR ta raba fetur Kyauta a Gombe
A Litinin din da ta gabata ne sashen kula da raba albarkatun man fetur na kasa DPR ta raba litar man fetur 300 kyauta ga masu ababen hawa a gidan Man Malullahi Global resources da ke garin Dadin kowa a Jihar Gombe. Da yake zantawa da manema labarai konturolan DPR na Gombe Abdullahi Abawa ne […]
A Litinin din da ta gabata ne sashen kula da raba albarkatun man fetur na kasa DPR ta raba litar man fetur 300 kyauta ga masu ababen hawa a gidan Man Malullahi Global resources da ke garin Dadin kowa a Jihar Gombe.
Da yake zantawa da manema labarai konturolan DPR na Gombe Abdullahi Abawa ne ya bayyana dalilin su na ba da man kyauta, kuma ya sa aka bude gidan man aka sayar a farashin gwamnati kan Naira 145.
Abdullahi Abawa, ya ce gidan Mai na Malullahi suna sayar da man ne kan Naira 210, sannan sun boye fiye da Lita dubu 26,800 da suke sayar wa ’yan bunburutu a jarkuna, kuma aka samu Lita 300 a jarkuna wadanda aka rabar kyauta.
Ya ce bayan sun sa a bude gidan man a sayar da kan farashin gwamnati da an gama za su rufe shi saboda karya doka.
Daga nan sai Abdullahi Abawa, ya kara da cewa nan gaba idan aka sake samun wannan gidan mai da irin wannan laifin za su janye lasisinsa.
Wani direba mai suna Muhammad Bello da muka zanta da shi, wanda ya samu mai na kyauta ya bayyana jin dadinsa kan yadda DPR ta ba su mai kyauta, wanda shi ma ya samu lita 30 da bai yi tsammani ba.
Muhammad Bello, ya kara da cewa tunda ya samu mai kyauta, shi ma zai sassauta wa fasinjoji wajen rage musu kudi, inda ya ce da wannan gidan mai yana sayar musu mai din kan Naira 220 ne.
Shi ma Babayo Abubakar, gode wa Allah ya yi da hukumar DPR kan wannan aiki da suke yi na samarwa da talaka sauki.
A lokacin wannan aiki DPR ta kulle gidajen mai uku saboda samun su da laifi na sayar da mai fiye da farashin gwamnati da kuma boyewa.
Cikin gidajen man da aka rufe sun hada da Barkidi Oil Nig ltd da ke Liji da gidan man Alhaji Hamidu Madu Mbahi da ke kwanar shiga garin Deba, sai gidan man Malullahi din da suka boye Lita dubu 26.