DR Congo: Sojoji sun ƙaddamar da gagarumin hari kan ’yan tawayen M23 —Shugaba Tshisekedi
Hare-haren mayaƙan M23 da ke samun goyon bayan ƙasar Rwanda sun kashe Gwamnan Birnin Goma, a makon jiya a yayin da dubban mutane ke gudun hijira domin tsira da rayukansu
Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, ya bayyana cewa sojojin ƙasar na tunkarar ’yan tawayen M23 da suka kaɗɗammar da munanan hare-hare tare da ƙwace ikon muhimman wurare a Birnin Goma da ke gabashin ƙasar.
Hare-haren mayaƙan M23 da ke samun goyon bayan ƙasar Rwanda sun kashe Gwamnan Birnin Goma, a makon jiya a yayin da dubban mutane ke gudun hijira domin tsira da rayukansu.
A ranar Laraba mayaƙan M23 suka ƙwace wasu yankuna biyu a Lardin Kivu da ke gabashin ƙasar, daga hannun sojoji.
A jawabinsa na ranar Laraba ta talabijin, Shugaba Tshisekedi ya zargi ƙasashen duniya kan rashin ɗaukar mataki kan lamarin, musamman hannun Rwanda a cikin lamarin, wanda ya ce katsalandan ne ga dimokuraɗiyya kuma yana iya ƙara munin al’amarin.
- NAJERIYA A YAU: Ainihin Dalilan Taƙaddama Kan Kafa Kotunan Musulunci A Kudu
- Za a dawo da ’yan Najeriya sama da 5,000 da ke zaune a Amurka
Ƙazancewar halin da ke ciki a Gabashin kasar ta DR Congo ya haifar da fargabar ƙara taɓarɓarewar yanayin rayuwar ’yan gudun da matsalar abubuwan more rayuwa a ƙasar.
Amma a ranar Laraba Shugaba Tshisekedi ya bayyana cewa ’yan tawayen suna ɗanɗana kuɗarsu a hannun sojojin ƙasar mai arziƙin zinare da lu’ulu da sauran ma’adinai.
Shugaba Felix Tshisekedi, a jawabinsa na farko tun bayan faruwar hare-haren na M23 a tsawon makonni, ya bayyana cewa sojojin sun samu gagarumar nasara.
Gabashin ƙasar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ya shafe shekaru sama da 30 yana fama rikici inda ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai ke addabar al’umma, baya ga tawaye ga gwamnati.
Ana alaƙanta wanna rikici da kisan kiyashi da aya auku a shekarar 1994 lokacin yaƙin basasa ƙasar Rwanda, maƙwabciyar DR Congo.