DSS sun tsare ’yan uwanmu wata 17 kan cinikin mota – Nuhu Kura
’Yan uwa da iyalan Ahmed Sakwaya da Garba Alhassan da ake zargin Hukumar DSS ta tsare sama da shekara daya ba tare da sanin inda suke ba, kuma ba tare da bayyana dalilin kama su ba a wajen sana’arsu, sun ziyarci Aminiya, inda suka bayyana cewa suna bukatar a sako musu ’yan uwansu ko a […]
’Yan uwa da iyalan Ahmed Sakwaya da Garba Alhassan da ake zargin Hukumar DSS ta tsare sama da shekara daya ba tare da sanin inda suke ba, kuma ba tare da bayyana dalilin kama su ba a wajen sana’arsu, sun ziyarci Aminiya, inda suka bayyana cewa suna bukatar a sako musu ’yan uwansu ko a gabatar da su a gaban kotu idan ana zarginsu da aikata laifi ne:
Da farko me ke tafe da ku?
Sunana Alhaji Nuhu Abubakar Kura, wan Alhaji Garba Alhassan, abin da ke tafe da mu mun kawo kuka ne kan ’yan uwanmu kannenmu da aka kama, wato Ahmed Sakwaya da Garba Alhassan. Jami’an Hukumar DSS ne suka kama su a wajen harkokinsu na sayar da motoci, a Unguwar Gama a Karamar Hukumar Nasarawa, Jihar Kano. Suna sayar da motocin ne a ofishinsu da ke U&M Motors a Lamba 14, kan Titin Katsina kusa da tsohuwar NEPA da NITEL, a Karamar Hukumar Fagge a Kano. Ina gida aka zo aka fada min abin da ya faru, sai na tafi gidan kanena na tambaye su, suka ce su ma ba su san abin da yake faruwa ba amma ya bugo musu waya ya ce wata rigima ta hada su da wani mutum ana ace masa Mallah sai DSS suka zo suka kama su, suka ce za su je gaban DSS, gobe idan an warware maganar za su dawo gida. Sai na koma wajen mutumin da ya min Allah kyauta, sai ya fada min ai Hukumar DSS ne suka zo wajensu saboda akwai wani mutum da ake kira Mallah, DSS sun kama shi, ya ba Alhaji Garba kudi Naira dubu 380. To kwana 22 da kama Alhaji Garba, na je na yi wa Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II magana cewa, an kama dan uwana har yanzu ban gan shi ba. Sarkin ya hada ni da Wali aka kira DSS na gidan Sarki da suka yi wa DSS na Unguwar Giginyu magana a kan abin da yake faruwa, suka ce ba shakka su suke da ruwa wajen kama Garba Alhassan da Ahmed Sakwaya saboda haka sai an yi bincike za a sako su. Yau Alhamis 13 ga watan Disamba 2018 da wannan magana wata 17 da kwana 10. Kuma duk in na je wajensu a kan wannan magana sai su ce ana nan ana bincike, daga Allah ba mu da kowa sai gwamnati, saboda mun san wannan gwamnati mai adalci ce ta taimaka mana, idan har wadannan mutane sun mutu a ba mu gawarsu, idan kuma ba su mutu ba a nuna mana su, ko a ba mu su.
Me suka yi aka kama su?
Jami’an tsaro na DSS Ba su fito sun fada mana ko sun yi laifi ba, wannan abu an ce kawai bincike za a yi, ko kuma ga abin da ake tuhumarsu da shi.
A ina ne aka tsare su?
An ce a Abuja ne daga nan aka tura su Kano a Giginyu daga nan aka tura su Abuja da motocinsu guda biyu kirar Sienna, har yanzu ba motocin ba masu motocin. Babu wanda ya san inda suke saboda babu wanda zai saurare ka, tun lokacin da na je wajen Sarkin Kano ya hada ni da Walin Kano na je wajensu da dama, sai dai a ce ana bincike, su ba su ba ni hasken komai ba.
Su wane ne kuke zargi da hannu wajen kama ’yan uwanku?
Jami’an DSS, saboda lokacin da na je gidan Sarki an kira reshen ofishin DSS na Gingiyu, sun tabbatar da saninsu a kama su.