DSS ta bindige mukarraban Sunday Igboho

Hukumar ta cafke mabiyan Igboho 12, tana neman sa ruwa a jallo.

DSS ta bindige mukarraban Sunday Igboho

Makaman da DSS ta kwace a hannun mabiyan Igboho

Hukumar tsaro ta DSS ta bindige biyu daga cikin mukarraban mutumin da ke jagorantar korar Fulani daga yankin Kudu-maso-Yamma, Sunday Igboho.

DSS ta bayyana a ranar Alhamis da dare cewa ta cafke mabiyan Igboho 12 a yayin musayar wuta shi kuma tana ci gaba da neman sa ruwa a jallo, duk inda yake boye, sai ta kano shi

A yayin jawabi kan ayyukan Igboho, kakakin DSS, Peter Afunanya, ya ce mutum shida daga cikin mabiyan nasa na dauke da bindigogi kirar AK 47, wasu uku kuma ke dauke da bindigogi kirar Pump Action.

“A yayin dauki-ba-dadin ne aka kashe biyu daga cikin mabiyan na Igboho, sauran kuma aka ci karfinsu, aka kama su.

“Jami’i daya ne ya samu rauni bayan maharan sun harbe shi a hannunsa na dama, amma yana samun kulawa kuma yana cikin koshin lafiya.”