DSS ta cafke Abdulaziz Yari

Babu dai cikakken bayani kan makasudin tsare shi

DSS ta cafke Abdulaziz Yari

Tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari

Hukumar tsaro ta DSS ta cafke tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, kuma tana ci gaba da titsiye shi a hannunta.

Har zuwa yanzu dai babu cikakken bayani a kan makasudin kama Yari, wanda kuma shi ne Sanatan Zamfara ta Yamma mai ci.

A cewar wata majiya da ke da kusanci da dan majalisar, Yari ya kai kansa ne ofishin hukumar tun bayan kammala zaman majalisa ranar Alhamis.

Majiyar dai ta yi ikirarin cewa da ita aka raka Sanatan zuwa ofishin na DSS domin amsa gayyatar da suka yi masa.

“Har yanzu Sanata Yari yana hannun DSS, amma nan ba da jimawa ba zai fito Insha Allah. Da kansa ya je ofishin bayan kammala zaman majalisa. Ni na raka shi, kuma har yanzu yana hannunsu,” in ji majiyar, wacce ta bukaci a sakaya sunanta.

Sai dai majiyar ba ta bayyana ainihin makasudin gayyatar Sanatan ba.

Bayanai sun nuna an cafke shi ne bayan Shugaban hukumar, Yusuf Magaji Bichi, ya bukaci ya gaggauta zuwa hedkwatar hukumar domin wata tattaunawa ta gaggawa.

Sai dai har zuwa yammacin ranar Asabar, wayar tsohon Gwamnan a kashe take.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai hukumar ta DSS ba ta magantu ba a kan kamun.

A watan da ya gabata ne dai Yari ya tsaya takarar Shugabancin Majalisar Dattawa, inda ya fafata da Godswill Akpabio, wanda APC da Fadar Shugaban Kasa suke so a zaba.

Sai dai bayan an yi zabe, Yari ya sha kaye a hannun Akpabio.

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato