DSS ta cafke Babban Editan jaridar Al-Mizan
Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS sun cafke Babban Editan jaridar Al-Mizan ta mabiya Shi’a, Ibrahim Musa, a Kano. An kama shi ne a filin jiragen sama na Malam Aminu Kano da ke Kano a ranar Laraba, a kan hanyarsa ta tafiya kasar Saudiyya domin ibadar Umarah. An yi jana’izar mutum 6 da ’yan bindiga suka […]
Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS sun cafke Babban Editan jaridar Al-Mizan ta mabiya Shi’a, Ibrahim Musa, a Kano.
An kama shi ne a filin jiragen sama na Malam Aminu Kano da ke Kano a ranar Laraba, a kan hanyarsa ta tafiya kasar Saudiyya domin ibadar Umarah.
- An yi jana’izar mutum 6 da ’yan bindiga suka kashe a Zangon Kataf
- Gobara ta kashe mutum 100 a wajen bikin aure a Iraƙi
Jaridar Al-Mizan dai na fita ne kowanne mako a cikin harshen Hausa.
A cikin wata sanarwa da wani dan uwan mawallafin mai suna Abdullahi Usman ya fitar a ranar Laraba, ya tabbatar da kamun sannan ya bukaci a gaggauta sakin Ibrahim din.
Sanarwar ta ce, “Jami’an hukumar ba su bayar da kowanne irin dalili na kama shi ba, duk da sun san matsayinshi kan bukatar neman a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky, wanda gwamnati ta kama a Zariyan Jihar Kaduna a shekara ta 2015.
“An kama Ibrahim Musa ne, wand yake tare da wata ’yar uwarsa mai suna Binta Sulaiman, lokacin da DSS ta kama shi a filin na Kano da sanyin safiyar Laraba, a kan hanyarsa ta tafiya Umarah.”
Sai dai Abdullahi ya ce Ibrahim ya yi kaurin suna wajen sukar lamirin kisan da kuma nuna wariyar da ake yi wa mabiya Shi’a da suka ce gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta yi.
Sun kuma bukaci a gaggauta sakin shi ba tare da bata lokaci ba.