DSS ta cafke Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah Bello Bodejo
Sakataren kungiyar Miyetti Allah, Saleh Al-Hassan, ya tabbatar da kamen da aka yi.
Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS ta kama shugaban ƙungiyar Miyetti Allah, Bello Bodejo, kan kafa rundunar sa-kai ta Fulani a Jihar Nasarawa.
Bayanai sun ce an cafke Bodeje ne wannan Talatar a babban ofishin Miyetti Allah da ke Kasuwar Shanu a babbar hanyar Tudun Wada da ke Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasawara.
- Tinubu ya gana da Sakataren Harkokin Wajen Amurka a Abuja
- Kotu ta tsare Dan Bilki Kwamanda kan cin zarafin Kwankwaso
A ranar Laraba 17 ga watan Janairu Bello Badejo ya ƙaddamar da rundunar a garin Lafiya, inda ya ce za ta taimaka wajen yaƙar ɓarayi da ɓata-gari daga cikin Fulani
Wata majiyar DSS ta ce sun kama Bodejo ne kan fargabar cewa kirkiro da ƙungiyar sa-kai zai iya janyo tashin hankali a faɗin ƙasar, kuma kasancewar ba ta da rijista da hukumar ta DSS.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, jami’an DSS da wasu sojojin kasa ne suka yi wa babban ofishin na Miyetti Allah shigar ba-zata da misalin ƙarfe 3:40 na Yammacin ranar Talatar, inda suka your awon gaba da Bodejo bayan kama shi.
Sai dai an yi rashin sa’a a ƙoƙarin jin ta bakin mai magana yawun DSS, Dokta Peter Afunanya da ta tuntuba, wanda bai amsa kiran waya da sakon tes da aka aika masa ba.
Sakataren kungiyar Miyetti Allah, Saleh Al-Hassan, ya tabbatar da kamen da aka yi.