DSS ta dawowa da Ajaero fasfonsa
DSS ta sakin fasfo ɗin Ajaero biyo bayan sakinsa cikin daren ranar Litinin.
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), ta saki fasfo ɗin Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), bayan sakinsa cikin daren ranar Litinin.
Wasu daga cikin shugabannin ’yan ƙwadago sun bayyana wa Aminiya a ranar Talata, cewa DSS ba ta gano komai da ya alaƙanta Ajaero da ta’addanci ba.
Aminiya ta ruwaito cewa DSS ta fuskanci matsin lamba kafin bayar da belin shugaban ƙungiyar a ranar Litinin.
Idan ba a manta ba, DSS ta sako Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), Joe Ajaero, kimanin mintoci 35 kafin cikar wa’adin da ƙungiyar ta bayar.
A cikin dare ne dai hukumar ta sako Ajaero, a kan beli, gabannin cikar wa’adin ƙarfe 12 da ƙungiyar na sakin sa.
NLC da ƙungiyoyin ma’aikata sama a 50 da ke ƙarƙashinta sun yi barazanar yajin aiki da zanga-zangana faɗin Najeriya idan har 12 na dare yi ba a sako shi ba.
Kafin cikar wa’adin ne Ajaero ya sanar ta shafi da na X cewa, “Gwmanatin Tinubu ta sako shugaban NLC Ajaero daga ofishin DSS a kan beli,” in ji shi.
Jami’an NLC da masu rajin kare haƙƙin dan Adam da dama sun tabbatar da cewa DSS ta sako Kwamred Joe Ajaero.
Jami’an hukumar DSS sun kama Ajaero ne da sanyin safiyar Litinin din a filin jirgin sama da ke Abuja, a hanyarsa ta zuwa taron Ƙungiyar Ƙwadago ta Duniya a ƙasar Birtaniya.
Kwanaki 10 ke nan bayan ’yan sanda sun yi masa tambayoyi kan zargin ɗaukar nauyin ta’addanci, a ranar 29 ga watan Agusta.
NLC da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan Adam da dama, sun yi tir da lamarin tare da kira ga hukumar ta gaggauta sako shi.
Jim kaɗan da haka ne dai jami’an DSS suka kai wani samame ofishin ƙungiyar SERAP mai bibiyar kashe kuɗaɗen gwamnati da ke Abuja, suna neaman shugaban cibiyar.
Wannan dai ya jawo wa hukumar cacckar daga ƙungiyar Amnesty International, wadda ta ce matakin ya nuna Gwamnatin Tinubu ta wuce gona da iri.