DSS ta gayyaci dakataccen Shugaban EFCC, Bawa

DSS ta gayyace shi jim kadan bayan dakatar da shi daga shugabancin EFCC.

DSS ta gayyaci dakataccen Shugaban EFCC, Bawa

Hukumar Tsaro ta DSS ta gayyaci dakataccen Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hancin da Rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa.

Bawa ya isa ofishin na DSS sa’o’i kadan da bayan dakatar da shi da Shugaba Bola Tinubu ya yi a ranar Laraba.

“Gayyatar ta shafi wani bincike da ake yi a kansa,” in ji sanarwar da Kakakin DSS, Peter Afunanya, ya fitar a yammacin Laraba.

Wannan ci gaban ya biyo bayan amincewar da Shugaba Bola Tinubu ya yi na dakatar da Bawa domin ba da damar gudanar da bincike game da ofishinsa kan wasu zarge-zarge.

A cewar sanarwar da Daraktan Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey ya fitar, matakin ya biyo bayan zarge-zargen “masu girma” na cin zarafin ofishi da ake wa Bawa.

“An umarci Mista Bawa da ya gaggauta mika al’amuran ofishinsa ga Daraktan Ayyuka a Hukumar, wanda zai kula da harkokin ofishin har zuwa lokacin kammala binciken,” in ji sanarwar.

A makon da ya gabata ne shugaba Tinubu ya dakatar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Bayan dakatar da Emefiele, DSS ta yi awon gaba da shi a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Jihar Legas.

A ƙofar banɗakin Gidan Yarin Kuje nake kwana — Ɗan zanga-zanga

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7