DSS ta gurfanar da Emefiele gaban kotu
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce ta gurfanar da dakataccen Gwamnan Babban Bankin Ƙasa Godwin Emefiele a gaban kotu. Wannan ya biyo bayan umarnin da wata Babbar Kotu a Abuja ta bayar ranar Alhamis cewa ko dai DSS ta gurfanar da Mr. Emefiele cikin mako guda ko kuma ta sake shi. Ƴan sa’o’i […]
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce ta gurfanar da dakataccen Gwamnan Babban Bankin Ƙasa Godwin Emefiele a gaban kotu.
Wannan ya biyo bayan umarnin da wata Babbar Kotu a Abuja ta bayar ranar Alhamis cewa ko dai DSS ta gurfanar da Mr. Emefiele cikin mako guda ko kuma ta sake shi.
Ƴan sa’o’i bayan wannan umarnin ne, kakakin DSS Peter Afunanya ya ce an gurfanar da Emefiele bisa biyayya ga umarnin kotun.
Ta’asar da Shugaban INEC ya tafka ta fi ta Emefiele – Buba Galadima
Godwin Emefiele yana hannunmu — DSS
Sai dai bayyana kotun da aka gurfanar da shi ba ko tuhumar da aka yi masa gaban kotun.
Ranar Juma’a 9 ga Yunin 2023 ne shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele daga muƙaminsa na Gwamnan Babban Bankin ƙasa.
Washegari kuma DSS ta sanar da cewa Mr. Emefiele ya shiga hannunta.
Sai dai babban lauyan nan mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana, SAN ya shawarci DSS da bar EFCC ta gurfanar da Emefiele gaban kotu kasancewar ana zarginsa ne da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa.
Mr Falana ya ce kamata ya yi da zarar DSS ta kammala bincike ta tura Mr Emefiele zuwa ga EFCC.