DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci
A baya an taɓa kama Mahdi Shehu kan yaɗa bayanan ƙarya a shafukan sada zumunta.
Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), ta gurfanar da fitaccen mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam daga Jihar Kaduna, Mahdi Shehu, kan zarge-zargen da suka shafi ta’addanci guda biyar.
Sun gurfanar da shi kan ayyukansa na kafafen sada zumunta da kuma wasu ayyuka na daban.
- Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda
- Rabon Awaki bai dace da Gwamnan Kano ba — Jaafar Jaafar
An sake kama Shehu a makon da ya gabata a asibitinsa da ke Kaduna, kwanaki biyu kafin DSS ta shigar da kara a Babbar Kotun Tarayya.
A watan Disamban 2024, an taɓa kama shi saboda yaɗa wani bidiyo da ya yi iƙirarin cewa Gwamnatin Najeriya ta bai wa Faransa damar kafa sansanin soji a Arewaci.
Ko da yake kotu ta bayar da belinsa a watan Janairun 2025, DSS ta sake samun izinin kotu na tsare shi na tsawon kwana 60 domin ci gaba da bincike.
Zarge-zargen da aka yi masa sun haɗa da yaɗa bayanan ƙarya, tayar da hankalin jama’a, da kuma amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa abubuwan da suka shafi barazanar tsaron ƙasa.