DSS ta kama buhu 2,000 na shinkafar tallafin da aka karkatar a Katsina

Jami’an DSS sun iske shagunan mutanen cike da shinkafar tallafin d a Gwamnatin Tarayya ta bayar a raba wa talakawan jihar

DSS ta kama buhu 2,000 na shinkafar tallafin da aka karkatar a Katsina

Hukumar tsaro ta DSS ta kama sama da buhu 2,000 na shinkafar tallafin Gwamnatin Tarayya ta bayar a raba wa talakawa a hannun wasu da ake zargin sun karkatar ne a Jihar Katsina.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan Gwamnatin Tarayya ta ba da tirela 20 na shinkafa domin raba wa talakawa, da nufin rage musu radadin yunwa da tsadar rayuwa.

Jami’an DSS sun kama wadanda ake zargin sun karkatar da shinkafar da ya kamata a raba wa talakawan jihar ne a Babbar Kasuwar Katsina.

A daren ranar Laraba ne DSS ta kama ’yan kasuwan da ake zargi, inda jami’an hukumar suka iske shagunan mutanen cike da shinkafar tallafin.

Wasu dai na zargin ba za a rasa  hannun wasu jami’an gwamnati a wannan badakalar ba.

Gobarar Tankar mai: Gwamnatin Kano ta ba da gudunmawar N100m ga Jigawa

An kama ɗan sandan ƙarya a Kano

Zargin kwartanci: Hisbah ta kama kwamishina da matar aure a Jigawa

Fashewar tankar mai: Mamata sun ƙaru zuwa 170