DSS ta kama jami’in hukumar agaji na bogi

Hukumar tsaro ta DSS ta kama wani mutum da aka gano yana jagorantar wata ƙungiya mai zaman kanta mara rajista a yankin Neja Delta. Mista Kennedy Tabukoi, ya shiga hannu ne kan amfani da kungiyar bunƙasa yankin Neja Delta (NDDI), wajen yi wa wasu manyan mutane da jami’an gwamnati zagon ƙasa. Wani jami’in DSS da […]

DSS ta kama jami’in hukumar agaji na bogi

Hukumar tsaro ta DSS ta kama wani mutum da aka gano yana jagorantar wata ƙungiya mai zaman kanta mara rajista a yankin Neja Delta.

Mista Kennedy Tabukoi, ya shiga hannu ne kan amfani da kungiyar bunƙasa yankin Neja Delta (NDDI), wajen yi wa wasu manyan mutane da jami’an gwamnati zagon ƙasa.

Wani jami’in DSS da ya shaida mana cewa an damƙe Tabukoi ya bayyana cewa hukumar ta gano cewa wanda ake zargin na da hannu wajen kista wasu zanga-zangar fafutikar adawa da gwamnati a yankin Neja Delta.

“Duk lokacin da jami’an gwamnati suka ki biya masa buƙata sai ya tunzura wasu kungiyoyi su yi bore da tattakin adawa da su.”

Ya ce, jami’an tsaro sun daɗe suna neman Mista Tabukoi, bayan wasu jami’an gwamnati sun kai ƙara kan yadda yake musu barazana idan ba su ba shi wasu maƙudan kuɗaɗe ba.”

A ranar Alhamis Mista Tabukoi ya jagoranci wata zanga-zangar ƙungiyoyin yankin Neja Delta a kofar Majalisar Dokoki ta Ƙasa kan zargin rufa-rufa a ɓangaren man fetur.

Tabukoi na zargin ’yan majalisar dokokin ta ƙasa da yunƙurin daƙile bincike a ɓangaren man fetur.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe