DSS ta kama mai baiwa masu garkuwa da Boko Haram magunguna

Hukumar tsaro ta cikin gida (DSS) ta ce, jami’anta sun kama wani mai suna Yusuf Salisu wanda suke zargin mai baiwa masu garkuwa da jama’a magunguna ne da kuma mayakan Boko Haram. An kama wanda ake zargin ne a ranar 9 ga watan Nuwamba 2019 a kauyen Sabon Birni da ke Karamar Hukumar Igabi a […]

DSS ta kama mai baiwa masu garkuwa da Boko Haram magunguna

Hukumar tsaro ta cikin gida (DSS) ta ce, jami’anta sun kama wani mai suna Yusuf Salisu wanda suke zargin mai baiwa masu garkuwa da jama’a magunguna ne da kuma mayakan Boko Haram.

An kama wanda ake zargin ne a ranar 9 ga watan Nuwamba 2019 a kauyen Sabon Birni da ke Karamar Hukumar Igabi a jihar Kaduna. Kakakin Hukumar DSS Peter Afunanya ne ya sanar da hakan.

Afunanya, ya kara har zuwa lokacin da aka kama wanda ake zargin yana da shagon magunguna. Kuma yana da alaka da manyan Kwamandoji 13 na Boko Haram da hukumomin tsaro ke nema ruwa ajallo.