DSS ta kama mai damfarar jama’a da sunan Aisha Buhari

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gabatar da wata mata mai suna Amina Mohammmed a kan zargin amfani da fadar shugaban Najeriya domin damfarar mutane. A cewar hukumar DSS matar tana shiga cikin fadar shugaban kasa ba tare da izini ba. Kakakin hukumar DSS, Peter Afunaya, ya ce matar ta rika shiga cikin gidan […]

DSS ta kama mai damfarar jama’a da sunan Aisha Buhari

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gabatar da wata mata mai suna Amina Mohammmed a kan zargin amfani da fadar shugaban Najeriya domin damfarar mutane.

A cewar hukumar DSS matar tana shiga cikin fadar shugaban kasa ba tare da izini ba.

Kakakin hukumar DSS, Peter Afunaya, ya ce matar ta rika shiga cikin gidan matar shugaban kasa Aisha Buhari. Ya  kuma ce Amina ta damfari wani mai suna Alexander Chika Okafor  da aka fi sani da Chicason Naira miliyan 150 da sunan Aisha Buhari.