DSS ta kama matashi kan zargin safarar makamai a Kano
An kama matashin ne yayin da yake ƙoƙarin safarar wasu makamai zuwa Jihar Katsina.
Jami’an hukumar DSS
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama wani matashi da ake zargi da safarar makamai a Ƙaramar Hukumar Gezawa da ke Jihar Kano.
An kama wanda ake zargin, Muhammad Abubakar mai shekaru 30, yayin da ƙoƙarin safarar makamai ga ’yan bindiga a Jihar Katsina.
- 12 Ga Yuni: Har yanzu dimokuraɗiyyar Najeriya na fuskantar barazana — PDP
- Elon Musk ya zama na farko da dukiyarsa ta haura tiriliyan
Jami’an tsaro sun ce an samu bututun RPG guda huɗu a jikinsa, bindiga ƙirar AK-47 guda uku, da kuma harsasai.
Bincike ya nuna cewa ya karɓi makaman ne daga hannun wani mutum mai suna Bello a Ƙaramar Hukumar Maigatari da ke Jihar Jigawa, kuma an yi alƙawarin biyansa Naira 450,000 idan ya kai su Funtua a Jihar Katsina.
Majiyoyin tsaro sun ce kama shi ya samu nasara ne biyo bayan samun bayanan sirri da ake yi domin daƙile yaɗuwar makamai a jihohin Arewacin Najeriya.
DSS ta ce wannan mataki ya hana makaman isa hannun ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa DSS bisa wannan nasara, inda ya ce wannan babban ci gaba ne a yaƙi da ta’addanci.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamnan ya jinjina wa jami’an tsaro bisa ƙwarewa da suka nuna, yana mai cewa haɗin kai da musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen magance matsalar tsaro.
Gwamnan ya kuma sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro, tare da kira ga al’umma su kasance masu lura da bayar da sahihan bayanai ga hukumomi.
Ya ce yana da ƙwarin gwiwa bincike zai kai ga cafke sauran da ke da hannu wajen safarar makaman.