DSS ta kama tsohon ministan Tinubu, Uche Nnaji
Lamarin ya dauki sabon salo ne bayan da Nnaji ya zama dan takarar gwamnan Jihar Enugu na jam’iyyar PDP a zaben 2027.
Jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), sun kama Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, da safiyar ranar Laraba a Filin Jirgin Saman Akanu Ibiam da ke Jihar Enugu.
An kama Nnaji ne, yayin da yake shirin shiga wani jirgi domin zuwa Abuja.
- Mutum 100,000 sun mutu a rikicin da ya dabaibaye Myanmar bayan juyin mulkin 2021
- Kwamishinan zaɓen Neja ya shafe wata 9 a hannun mahara duk da biyan kuɗin fansa N40m
Majiyoyin tsaro sun ce DSS ta kama shi ne bisa umarnin Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC).
Bayan kama shi, an mika shi ga hukumar domin ci gaba da bincike.
A cewar majiyoyin, ICPC na binciken zargin da ake yi cewa Nnaji ya yi amfani da takardun shaidar kammala karatu na bogi.
Haka kuma, hukumar ta gayyace shi sau da dama bayan samun korafe-korafe kan yadda ya gudanar da Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha, kafin daga bisani ta nemi taimakon DSS wajen kama shi.
Nnaji, ya yi murabus daga mukaminsa na minista a ranar 7 ga watan Oktoba, 2025, bayan ce-ce-ku-ce ya barke kan takardun shaidar karatunsa na Jami’ar Nsukka (UNN) da kuma na shaidar kammala NYSC.
Bayan murabus dinsa, ya ce matakin nasa ba yana nufin amsa zargin da ake masa ba ne, face bai wa hukumomi damar gudanar da bincikensu bisa doka da oda.
Nnaji, ya kuma bayyana zarge-zargen a matsayin yarfen siyasa.
A watan Nuwamban 2025, ya shigar da kara a Babbar Kotun Tarayya yana neman a tilasta wa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka da Mataimakin Shugabanta, Farfesa Simon Ortuanya, su fitar masa da takardar bayanan karatunsa.
Ya ce jami’ar ta ki fitar masa da takardar duk da cewa bayanansa na karatu suna cikin sashen adana bayanai tare da na sauran daliban da suka kammala karatu a shekarar 1985, lamarin da ya sa ce-ce-ku-ce ya barke a kansa.
Lamarin ya dauki sabon salo ne bayan da Nnaji ya zama dan takarar gwamnan Jihar Enugu na jam’iyyar PDP a zaben 2027.