DSS ta kashe ’yan bindiga ta ƙwato buhunan makamai da kudade a Neja

An kama buhuna cike da abubuwa da ake kyautata zaton bindigogi ne da kuma tsabar kuɗi a hannunsu

DSS ta kashe ’yan bindiga ta ƙwato buhunan makamai da kudade a Neja

Hukumar tsaro ta DSS ta hallaka ’yan bindiga biyu tare da kama wasu da dama a ƙauyen Hayin-Nasara da ke yankin Tafa a Jihar Neja.

’Yan bindigar sun gamu da ajalinsu a hannun jami’an DSS ne a yankin da ke kan Babbar Hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Hukumar DSS ta ragargaji ’yan bibdigar ne a wani samame na musamman da ta kai a wasu rugagen Fulani da ke wajen garin Tafa a ranar Juma’a.

Wata majiya a DSS ta shaida wa wakilinmu cewa a yayin samamen an kama wasu buhuna cike da wasu abubuwa da ake kyautata zaton bindigogi da tsabar kuɗi, ne a cikin wani bukka.

Wani mazaunin ƙauyen Hayin-Nasara ya shaida mana cewa, “mun je mun gawar waɗanda ake zargin, shi kuma ɗayan, wanda ake wa laƙabi da ‘pointer’, jami’an tsaron sun tafi da shi.’’

Wani ɗan banga a yankin ya ce, Ya ce “Daga bayana sojoji sun zo daga Abuja suka ƙoƙƙonaa bukkoki da dama a rugar.”

A cewarsa, wasu daga cikin waɗanda ake zargin sun daɗe da zama a yankin.

Amma ya ce akwai waɗanda suka dawo kwanan nan domin su ɓuya sakamakon ragargazar da suke sha daga jami’an tsaro a daji.

Amma da muka tuntuɓi, Jami’in Hulɗa da Jama’a na ’yan sanda a Jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya shaida mana cewa ba shi da rahoto game da lamarin.