DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu

DSS ta buƙaci goge wani saƙo da Sowore ya wallafa wanda ta riƙa a matsayin na cin zarafi ta yanar gizo.

DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu

Hukumar Tsaron Farin Kaya a Nijeriya DSS, ta gurfanar da fitaccen ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore a kotu.

A ƙunshin ƙarar da DSS ta gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta haɗa da shafukan sada zumunta na X da kuma Facebook, inda take zarginsu da ba da ƙofar aibata Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Darekan shigar da ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, M.B Abubakar da wasu lauyoyi huɗu —M.E. Ernest da U.B. Bulla da C.S. Eze da kuma E.G. Orubor, ne suka shigar da ƙarar a madadin Gwamnatin Tarayya da kuma hukumar ta DSS.

DSS wadda ta kafa hujja da sashe na 24 da ke cikin kundin dokokin yanar gizo, ta ce Sowore ya yi amfani da shafukansa na dandalan sada zumunta na X da Facebook wajen wallafa wani saƙo da ke cin mutuncin Shugaba Tinubu.

Tun dai a farkon watan nan ne DSS ta buƙaci goge wani saƙo da ɗan gwagwarmayar ya wallafa wanda ta riƙa a matsayin bayanan ƙarya, cin zarafi ta yanar gizo da kalaman haddasa ƙiyayya, waɗanda kuma ta ce na iya haddasa rikici su kuma ɓata sunan Najeriya a ƙasashen waje.

Sai dai har zuwa ranar Litinin, 15 ga watan Satumba, babu wani mataki da aka ɗauka na goge saƙon da DSS ɗin ta buƙata.

Ana iya tuna cewa, a ranar 6 ga wannan wata na Satumba ne DSS ta bai wa shafin sada zumunta na X wa’adin sa’o’i 24 da ya goge wani saƙo da Soworen ya wallafa yana ƙaryata Tinubu.

A wasiƙar da DSS ta wallafa shafinta na X, ta zargi Mista Sowore da yin amfani da saƙonsa na X wajen cin fuskar shugaban ƙasa Tinubu da yi masa rashin mutunci da ba’a.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar 25 ga watan Agusta, Mista Sowore ya soki ziyarar da shugaban Nijeriya ya kai Brazil da kuma kalaman da shugaban ya yi yayin ziyarar.

A cikin saƙon, Sowore ya wallafa cewa, “Mai laifi @officialABAT [Bola Tinubu] ya kai ziyara Brazil inda ya ce babu cin hanci da rashawa a Nijeriya a gwamnatinsa. Ji wani ƙarfin hali na ƙarya da ko kunya babu!” in ji Omoyele Sowore (@YeleSowore) ranar 26 ga watan Agustan shekarar 2025.

A cikin wasiƙar da DSS ta aike wa kamfanin X ta ce waɗannan kalaman sun ɓata wa magoya bayan Shugaba Tinubu rai, lamarin da ya sa suka yi zanga-zangar rashin amincewa da kalaman na Sowore a kan titunan ƙasar.

Saboda haka, hukumar ta bai wa shafin X wa’adin sa’o’i 24 domin ya cire kalaman Sowore ko kuma ta ɗauki matakai masu tsauri a kan shafin.

Abin da Tinubu ya ce a Brazil

Ana iya tuna cewa dai a yayin ziyarar da Shugaba Tinubu ya kai ƙasar Brazil a watan jiya, ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ta yi a Nijeriya sun kawo ƙarshen cin hanci a ƙasar.

“Sauyen-sauyen da na ƙaddamar tun da na karɓi ragamar mulki a Nijeriya suna tasiri sosai. Zan iya bugun ƙirji kan haka. Daga farko sun ba da wahala. Amma a yau sakamakonsu yana haɓaka,” in ji Shugaba Tinubu.

“Yana daɗa bayyana ga mutane. Mun ƙara yawan kuɗi cikin tattalin arzikinmu. Yanzu babu cin hanci da rashawa. Gwamnan babban bankin [Nijeriya] ya zo nan. Ba sai ka san shi ba kafin ka samu takardun kuɗin ƙasashen waje da kake buƙata,” in ji shi.

Martanin Sowore

Shi kuwa Sowore, wanda hukumar DSS take ƙorafi game da saƙon da ya wallafa ya mayar da martani da saƙon DSS.

“Da safiyar yau, X (wanda a baya ake kira Twitter) ya tuntuɓe ni a hukumance game da wasiƙar barazana da suka samu daga hukumar DSS mara bin doka game da saƙon da na wallafa kan Tinubu. Ba zan goge saƙon ba,” in ji Sowore a saƙonsa na X.

Tun ba yanzu ba dai DSS ta yi gargaɗin cewa za a riƙe duk wani dandalin sada zumunta da bai cire saƙon da Sowore ya wallafa ba a matsayin wanda ke taimakawa wajen haddasa husuma, tana mai jaddada cewa da mawallafi da dandalin duk su na da laifi a ƙarƙashin dokokin Najeriya.