DSS ta nemi NLC ta janye zanga-zangarta kan tsadar rayuwa
Hukumar tsaro ta DSS ta bukaci kungiyoyin kwadago su janye zanga-zangar da suka shirya kan tsadar rayuwar da ke addabar ’yan Najeriya
Hukumar tsaro ta DSS ta bukaci kungiyoyin kwadago su janye zanga-zangar da suka shirya gunadarwa fadin Najeriya kan tsadar rayuwar da ke addabar ’yan Najeriya.
Hukumar ta DSS ta ce duk da cewa kungiyar na da hakkin gudanar da zanga-zangar a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu, amma rokon nata na neman zaman lafiya ne a fadin kasar da kuma kauce wa tada zaune tsaye.
Kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, ya bukaci shugabannin kungiyoyin kwadagon da su tattauna da jami’an gwamnati.
Bayan taronta na majalisar zartarwar kungiyar kwadagon ta kasa a Abuja ranar Juma’a ne suka sanar cewa za su gudanar da zanga-zangar kwanaki biyu a fadin kasar saboda gwamnati ta saba yarjejeniyoyin da suka cimma a watan Oktoban 2023.
- Kwastam za ta raba wa jama’a kayan abincin da ta kwace
- Ya kamata Hukumar Kwastam ta sakar wa ’yan kasuwa mara — Sarkin Kano
Sai dai Afunanya ya bayyana cewa zanga-zangar za ta kara tayar da hankali a kasar, yana mai cewa, a iya sanin hukumar DSS, gwamnati a dukkan matakai na kokarin ganin an daidaita yanayin tattalin arzikin, don haka ya kamata a yi la’akari da hakan.
Ya kuma yi zargin cewa wasu marasa kishi na shirin amfani da zanga-zangar wajen haifar da rikici a kasar don haka na jaddada bukatar sake yin tunani domin guje wa abin da zai kawo barazana ga zaman lafiya tare da mummunan sakamako.