DSS Ta Sake Gurfanar Da ‘Maitangaran’ Kan Kitsa Harin Boko Haram A Kano

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (DSS) ta sake gurfanar da wanda take zargi da kitsa hare-haren Boko Haram a Kano a shekarar 2014 a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja. Lauyan hukumar DSS, E.A Aduda, ya bayyanawa kotu cewa, hukumar ta sake gabatar da sabbin tuhume-tuhume kan wanda take zargin, kuma tana fatan […]

DSS Ta Sake Gurfanar Da ‘Maitangaran’ Kan Kitsa Harin Boko Haram A Kano

Tsohon hoto.

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (DSS) ta sake gurfanar da wanda take zargi da kitsa hare-haren Boko Haram a Kano a shekarar 2014 a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja.

Lauyan hukumar DSS, E.A Aduda, ya bayyanawa kotu cewa, hukumar ta sake gabatar da sabbin tuhume-tuhume kan wanda take zargin, kuma tana fatan kotun za ta yi duba a kan su.

Sai dai wanda ake zargin, Hussain Isma’ila, wanda aka fi sani da Maitangaran mai shekaru 34, ya musanta dukkan zargin da ake masa.

Lauyansa, Peter Dajang, ya bukaci kotun ya yi watsi da karar, saboda a ranar 6 ga watan Disambar 2021, kotu ta umarci DSS ta dauke Maitangaran daga wajen ta zuwa kurkukun Kuje domin ba shi damar ganawa da lauyoyinsa da kuma iyalin sa, amma har yanzu DSS ba ta bi umarnin kotu ba.

A nasa martanin, lauyan DSS ya ce hukumar ba ta bi umarnin kotun ba ne, saboda ta shigar da sabuwar bukata na janye batun mayar da shi kurkukun Kuje.

Alkalin kotun ya dage zaman zuwa 25 ga watan Janairu na sabuwar shekara, domin ci gaba da sauraron karar.