DSS ta saki tsohon shugaban EFCC, Abdulrashid Bawa
Kwanan shi 134 ke nan yana tsare a hannun DSS
Hukumar tsaro ta DSS ta saki tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC), Abdulrashid Bawa bayan shafe kwanaki 134 a tsare.
Bawa dai ya kasance a tsare tun a watan Yuni, lokacin da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya dakatar da shi daga kan kujerar shi.
A lokacin dai, Gwamnatin Tarayya ta ce ta dakatar da shi ne saboda a sami damar gudanar da cikakken bincike a kan zargin aikata almundahanar da ake yi masa.
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, kuma Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya zargi Bawa da neman cin hancin Dalar Amurka biliyan biyu daga hannun shi.
“Gaskiya ne, yau san sake shi bayan fuskantar matsin lamba daga wasu masu farcen susa a cikin jami’an tsaron kasar nan,” in ji wata majiya daga jami’an tsaro da ta bukaci a sakaya sunanta.
Kazalika, wata majiyar ta ce an sake shi bayan hukumar ta DSS ta kammala bincikenta a kan shi.