DSS ta sauke Babban Jami’in Tsaron Tinubu

Hukumar tsaro ta DSS ta janye Adegboyega Fasasi, Babban Dogarin Shugaban Kasa daga Fadar Aso Rock

DSS ta sauke Babban Jami’in Tsaron Tinubu

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta janye Babban Jami’in Tsaron Shugaban Kasa Bola Tinubu, Adegboyega Fasasi daga Fadar Shugaban Kasa.

Aminiya ta gano cewa DSS ta maye gurbin Fasasi da Rasheed Atanda Lawal, mai mukamin Mataimakin Darakta a hukumar, kuma tuni ya fara aiki a Fadar Shugaban Kasan.

Wasu majiyoyi a hukumar sun shaida mana cewa Fasasi wanda shi ne babban Jami’in Tsaron Shugaban Kasa tun da Tinubu ya hau mulki ya tafi kwas ne domin samun karin kwarewa.

Majiyar ta ce Darakta-Janar na hukumar, Tosin Ajayi ne ya aike wa Tinubu takardar neman izinin tura Fasasi kwas din saboda muhimmancinsa.

Masu masaniya kan yanayin aikin DSS sun bayyana cewa maye gurbin Fasasi da hukumar ta yi bakon abu ba ne, suna masu bayyana cwea shi kansa ya kamata ya san da hakan domin abu ne da aka saba yi a hukumar.

Majiyar ta bayyana cewa kasancewar sabon shugaban hukumar ya fara aiki, akwai yiwuwar ya sauya wa wasu wuraren aiki musamman wadanda ke da kusanci da Shugaban Kasa.

Majiyar ta ce, “Tabbas na ji an maye gurbinsa da wani saboda an tura shi wani kwas. To ai wannan shi ne dalilin cire shi da muka sani.

“Irin wannan sauyin wurin aiki ba sabon abu  ba ne a DSS musamman idan sabon Darakta-Janar ya fara aiki.

“Aikinsu na sirri ne da binciken kwakwaf, saboda haka kowane shugaban hukumar zai so ya nada mutanen da ya fi aminta da su a muhimman wurare da Fadar Shugaban Kasa, kuma na farko shi ne Ofishin Babban Jami’in Tsaron Shugaban Kasa”, in ji majiyar.

Sai dai har zuwa lokacin da muka kammala wannan rahoto babu wata sanarwa ko bayani a hukumance daga DSS game da lamarin.