DSS ta tabbatar da tsare Baffa Hotoro kan batanci ga Annabi

Hukumar ta ce Baffa Hotoro yana hannunta, bayan a baya ya karyata cewa hukumar ta kama shi kan zargin batanci ga Manzon Allah (SAW)

DSS ta tabbatar da tsare Baffa Hotoro kan batanci ga Annabi

Hukumar tsaro ta DSS ta ce tana tsare da matashin malamain nan da ake zargi da yin batanci ga Manzon Allah (SAW) a Jihar Kano, mai suna Baffa Hotoro.

Hakan na zuwa ne bayan a watan da ya gabata Ma’aikatar Harkokin Addinai na Jihar Kano ta sanar cewa DSS  ta tsare Baffa Hotoro da abokinsa, Habib Haroun (Abu Aaman), bisa zargin munana lafazi ga Annabi Muhammad (SAW).

Bayan sanarwar matashin ya fito a wani bidiyo ya karyata kama shi, inda ya ce yana Umara a lokacin; Amma a ranar Alhamis hukumar ta ce matashin yana hannunta.

A baya dai, Kwamishinan Harkokin Addinai na Jihar Kano, Ustaz Muhammad Nazifi Bichi, ya shaida wa Aminiya cewa sun karbi korafe-korafen zargin batanci a kan matasan malaman, wanda hakan ya sa hukumar ta sanar da DSS don daukar matakin da ya dace.

A cewar Daraktan, sun lura cewa rayuwar malaman ma tana cikin hatsari don haka ya zama dole su shiga cikin lamarin.

Baffa Hotoro ya ce kalaman malamin suna kan daidai, har ma ya kara da nasa, lamarin da ya janyo al’ummar jihar suka rubuta takardun korafi a kansa tare da neman hukumomi su shiga cikin lamarin.

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja