DSS ta tsare Gwamnan CBN bayan Tinubu ya dakatar da shi

Tinubu ya ba da umarnin a binciki za Emefiele, wanda ya dakatar ba tare da bata lokaci ba

DSS ta tsare Gwamnan CBN bayan Tinubu ya dakatar da shi

Hukumar Tsaro ta DSS ta tsare Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, jim kadan bayan Shugaba Tinubu Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shi.

Majiyoyinmu a DSS sun shaida mana cewa Emefiele yana tsare a ofishin hukumar “yana amsa tambayoyi” a daren Juma’a.

Aminiya ta ruwaito cewa Shugaban Tinubu ya dakatar da Emefiele, daga aiki ba tare da bata lokaci ba, tare da ba da umarnin a bincike shi, ta wata sanarwa da ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya fitar a daren Juma’a.

Sanarwar da Daraktan Yada Labarai, Willie Bassey ya fitar ta ce hakan ya biyo bayan binciken da ake yi a ofishin Emefiele da kuma sauye-sauyen da ake shirin yi a fannin hada-hadar kudi da tattalin arzikin Najeriya.

“An umarci Mista Emefiele da ya gaggauta mika al’amuran ofishinsa ga mataimakinsa, wanda zai yi aiki a matsayin mukaddashin Gwamnan CBN har sai an kammala bincike.”

Ana iya tuna cewa, bayan rantsar da Tinubu a ranar 29 ga watan Mayun 2023, ya gana da Emefiele a Fadar Shugaban Kasa, a ranar da shugaban ya fara shiga ofis.

Majiyoyinmu masu tushe sun shaida mana cewa daga cikin dalilan dakatar da Emefiele, har da rawar da ya daka wajen sauyin takardun kudi mai cike da rudani, da kuma dokar takaita cirar tsabar kudi da suka nemi kawo wa zaben 2023 da Tinubu ya lashe tarnaki.

Emefiele dai ya sha musanta zargin da ake masa, inda ya dage da cewa yana gudanar da aikinsa ne yadda dokar kasa ta tsara.

Kokarinmu na samun Emefiele ko kakakin CBN, Isa Abdulmumin ya ci tura; haka shi ma kakakin DSS, Peter Afunanya. Ko da yake, shi wayarsa ta shiga amma babu amsa, kuma mun tura masa rubutaccen sako, amma har muka kammala wannan rahoton ba mu samu amsa ba.

Ana iya tunawa cewa a lokacin yakin neman zabe, Tinubu ya yi zargin cewa an bullo da sabbin tsare-tsaren kudin ne domin yi masa kafar ungulu, amma hakan ba zai hana shi kai bantensa ba.

Emefiele ya nemi takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC — wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce — amma Tinubu ya kayar da shi a zaben fidda gwani.

Da ma ana  neman Emefiele

Wasu majiyoyinmu dai sun ce dama tun kafin saukar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kamata ya sallami Emefiele, amma bai yi ba.

Sun bayyana takaici bisa halin ko-in-kula na Buhari, duk da abin da suka kira kwararan hujjojin da aka gabatar masa da suka tabbatar da laifin karkatar da kudade da ake zargin Emefiele.

An kuma gano cewa hukumar DSS da EFCC da wasu hukumomin kula da hada-hadar kudi na gida da kasashen waje na neman Emefiele domin ya amsa tambayoyi.

Daga: Muideen Olaniyi da Abbas Jimoh da Abubakar Muhammad da Sagir Kano Saleh da