DSS za ta fara kerawa da sayar da jirage marasa matuka

Shugaban hukumar DSS, Yusuf Bichin ya ce nan ba da jimawa ba, za a kaddamar da makaman da jami’an hukumar suka kera.

DSS za ta fara kerawa da sayar da jirage marasa matuka

Hukumar tsaro ta DSS ta ce tana shirin fara kerawa da sayar da jirage marasa matuka ga sauran hukumomin tsaron Najeriya.

Daraka-Janar na hukuar DSS, Yusuf Bichin ya ce nan ba da jimawa ba, za a kaddamar da makaman da jami’an hukumar suka kera.

Shugaban hukumar ya sanar da haka ranar Asabar a bikin yaye malarta kwas din binciken kwakwaf a babban matakin gudanarwa.

Hakan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ce-ce-ku-ce bayan wani jirgi mara matuki na Rundunar Sojin Kasa ta kasar ya jefa wa farare hula bom ya kashe mutane 120 bisa kuskure.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja