Duba gari sun kulle masallaci a Legas

Hukumar kula da tsabtar gari ta Jihar Legas ta kulle wani masallaci a unguwar Marina a bisa dalilan rashin tsabtar makewayinsa.  A cewar babban manajan hukumar, Dakta Samuel Adejare, ya zame wa hukumar tilas ta rufe masallacin duk da cewa wajen ibada ne da aka gina na wucin-gadi a saboda ma’aikatan yankin domin kazantar makewayin […]

Duba gari sun kulle masallaci a Legas
Duba gari sun kulle masallaci a Legas

Hukumar kula da tsabtar gari ta Jihar Legas ta kulle wani masallaci a unguwar Marina a bisa dalilan rashin tsabtar makewayinsa. 

A cewar babban manajan hukumar, Dakta Samuel Adejare, ya zame wa hukumar tilas ta rufe masallacin duk da cewa wajen ibada ne da aka gina na wucin-gadi a saboda ma’aikatan yankin domin kazantar makewayin masallacin ya kai matuka. Bututun ban dakin na zubar da kashi a magudanan ruwa, wanda hakan kan yi illa ga lafiyar mutanen yankin. Ya kuma sha alwashin ci gaba da sanya ido a kasuwanni da gine-gine da wuraren ibadaa domin tabbatar da tsabtarsu, kana ya yi ikirarin kulle duk inda aka samu da keta doka; domin a cewarsa hukumar ba za ta lamunci kazanta ba.
Tuni dai Gwamnan Jihar Ogun mai makwabtaka da Legas, Sanata Ibikunle Amosun ya yi ta yin rangadi a watanni 2 da suka shude, inda ya yi ta shiga loko da sako da ke ilahirin jihar don gane wa idanunsa yadda jama’a ke kula da tsabtar muhalinsu; inda ya sa aka rufe kasuwanni da gidaje da dama da ya bayyana su da kazanta, kafin daga bisani ya ba da izinin sake bude su bayan an tsaftace su.