Duba wayar miji ba izini ya jawo wa wata mata dauri a kurkuku
Kotun ta daure matar na tsawon wata uku saboda bincikar wayar mijinta.
Wata kotu a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta yanke wa wata mata hukuncin daurin wata uku a kurkuku saboda duba wayar mijinta, ba tare da izininsa ba.
Mijin ya maka matar tasa a kotu ne inda ya zarge ta da duba wayarsa ba tare da izininsa ba, inda ya bukaci kotun ta bi masa kadinsa.
Kotun da ke yankin Ras a Al-Khaima ta sami matar da laifin keta sirrin mijin nata.
Kazalika, an tuhume ta da kwafar bayanai, hotuna da tattaunawarsa da wasu abubuwan ta wasu manhajoji.
Daga nan ne kotun ta yanke mata hukuncin biyan tarar kudi AED 8,100, bayan samunta da laifi.
Sai dai matar ta ce tana zargin mijin nata na cin amanarta ne, wanda shi ne dalilin da ya sa ta binciki wayar tasa.
Kasar UAE dai ta yi kaurin suna wajen kafa dokoki masu tsauri, musamman wanda suka shafi sha’anin aure da zamantakewa.