Dubban jama’a suka tarbi Sarkin Kazaure

Dubban jama a suka yi dafifi domin tarbar Mai martaba Sarkin Kazaure Alhaji Najeeb Husaini Adamu lokacin da ya dawo gida daga jinyar da ya yi a kasar Ingila na tsawon wata uku, inda masoya da ’yan uwa da abokan arziki suka yi wa gadar Kazaure cikar kwari don murnar dawowarsa.A lokacin da Sarkin yake […]

Dubban jama’a suka tarbi Sarkin Kazaure

Dubban jama a suka yi dafifi domin tarbar Mai martaba Sarkin Kazaure Alhaji Najeeb Husaini Adamu lokacin da ya dawo gida daga jinyar da ya yi a kasar Ingila na tsawon wata uku, inda masoya da ’yan uwa da abokan arziki suka yi wa gadar Kazaure cikar kwari don murnar dawowarsa.
A lokacin da Sarkin yake jawabi ga dubban jama’ar da suka taru a fadarsa, ya yi wa Allah godiya da Ya dawo da shi lafiya kuma ya yi alkawarin ci gaba da taimaka wa jama’ar masarautarsa su samu abubuwan more rayuwa.
daya daga cikin hakiman Sarkin wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana dawowar Sarkin gida da cewa alheri ne ga masarautar da jama’arta inda babu abin da za su ce sai godiya ga Allah kan dawo musu da Sarkin lafiya.
Ya ce jama’ar masarautar Kazaure suna kaunar sarkinsu ne saboda irin mulkin adalci da yake gudanarwa ga jama’ar masarautar ba tare da nuna bambanci ba.
Wani na hannun damar Sarkin Alhaji Abubakar Mu’azu Adamu ya nuna matukar jin dadinsa kan yadda al’ummar masarautar suka nuna wa dan uwansa kauna, ya ce hakika tarbar da jama’a suka yi wa Sarkin tun a Kano zuwa gadar Kazaure ya nuna cewa Mai martaba yana zaune lafiya da jama’a.
 Ya ce taron da aka yi na tarbar Sarkin tamkar na Ranar Sallah ne inda kusan kowa da kowa ya fito.
Maroka da mawaka da ’yan algaita sun baje kolinsu wurin ruguntsumin barka da dawowar Sarkin ta yadda wani ba ya jin na wani.