Dubban jama’a sun tarbi Sarkin Yawuri bayan dawowarsa daga Umara
Dubban jama’a ne suka tarbi Mai martaba Sarkin Yawuri Alhaji Muhammadu Zayyanu Abdullahi bayan dawowarsa daga Saudiyya.A makon jiya ne Mai martaba Sarki Zayyanu Abdullahi ya dawo gida Najeriya bayan shafe makonni a kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Umara, inda dubban jama’ar kasar Yawuri suka yi dandazo a garin Tondi-Gada inda suka tarbe shi […]
Dubban jama’a ne suka tarbi Mai martaba Sarkin Yawuri Alhaji Muhammadu Zayyanu Abdullahi bayan dawowarsa daga Saudiyya.
A makon jiya ne Mai martaba Sarki Zayyanu Abdullahi ya dawo gida Najeriya bayan shafe makonni a kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Umara, inda dubban jama’ar kasar Yawuri suka yi dandazo a garin Tondi-Gada inda suka tarbe shi cikin farin ciki da nuna kauna ga shugaba kuma uba ga al’ummarsa.
A cikin wadanda suka tarbi Sarkin har da Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Ibrahim K. Aliyu, Matawallen Yawuri da Shugaban Ma’aikata na Jihar Alhaji Babale Umar Yawuri da sauran manyan ma’aikatan tarayya da jiha da na kananan hukumomi da sarakunan gargajiya da daruruwan jama’ar masarautar.
A cikin jawabin da Mai martaba Sarkin ya gabatar, ya nuna farin cikinsa kan kauna da soyayyar da jama’ar masarautar suke nuna masa, inda ya yi wa jama’a fatar alheri da zaman lafiya mai dorewa a masarautar da jihar da kuma kasa baki daya.