Dubban Musulmi sun halarci bikin Mauludi na Ibadan

Kamar kowace shekara, a bana ma al’ummar Musulmi maza da mata daga jihohi shida na Kudu maso Yamma sun hadu a birnin Ibadan, inda suka yi kwana- zaune tare da jerin gwanon suna tafiya a kasa suna rera wakoki da kidan Bandiri domin nuna murna da farin cikin zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (SAW). Sannan […]

Dubban Musulmi sun halarci bikin Mauludi na Ibadan

Kamar kowace shekara, a bana ma al’ummar Musulmi maza da mata daga jihohi shida na Kudu maso Yamma sun hadu a birnin Ibadan, inda suka yi kwana- zaune tare da jerin gwanon suna tafiya a kasa suna rera wakoki da kidan Bandiri domin nuna murna da farin cikin zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (SAW).

Sannan masallatai da dama sun cika makil da dubban Musulmi a Unguwar Sabo, Ibadan, inda mabiya darikun Kadiriyya da Tijjaniya daga makarantun Islamiyya da kungiyoyin Musulunci suka yi mauludin kuma suka raba wa jama’a abinci don nuna murnarsu da zagayowar wannan rana.

Khalifan Darikar Kadiriyya, Sheikh Munzali Ummar Mai Bandiri da Khalifan Darikar Tijjaniya Sheikh Ibrahim Inuwa ne suka jagoranci daruruwan mukaddamai da manyan malamai tare da  dimbin mabiyansu a wannan sashe wajen yin zagayen na ranar Talata wanda aka shafe awoyi 5 ana yi. Bayan kammala zagayen ne malaman suka koma masallatai da gidajensu suka ci gaba da fadakar da jama’a kan abubuwa da dama na addini.

Cikin sakonsa ga al’ummar Musulmin, Sheikh Munzali Umar Mai Bandiri ya ce, “Ina yin kira ga dukan ’yan uwa Musulmi mu yawaita bautar Ubangiji kuma mu guje wa ayyukan sabon Allah domin suna janyo aukuwar masifu, kuma mu girmama shugabanni mu daina yin kalaman batunci da zage-zage ga na gaba da mu kuma mu tashi tsaye wajen ilimantar da ’ya’yanmu kan addinin Musulunci sannan mu yawaita yin addu’ar Allah Ya samar da zaman lafiya a kasarmu.”

Shi kuwa Sheikh Ibrahim Inuwa  cewa ya yi “Da farko ina rokon ’yan uwana da muke zaune a wannan sashe mu  kyautata zamantakewarmu da jama’ar garuruwan da muke zaune kuma mu girmama dokokin mahukunta domin samar da zaman lafiya a Jihar Oyo da kasa baki daya. Kuma ina kira ga Musulmi a ko’ina suke a duniya su rika sadaukar da rayuka da dukiyarsu wajen girmama irin wannan rana da muke yin Maulidi don murnar  haihuwar Annabi Muhammad (SAW).”

Wakilinmu ya ce zagayen ta bana ta kayatar, domin manya da yara sun yi ta cikin shauki da murnar zagayowar wannan rana kuma an gudanar da komai lami lafiya.