Dubban tsuntsaye suka shiga gasar wake-wake

  An fara gasar wakar tsuntsaye a kudancin Narathiwat  a kasar Thailand. Tsunsaye dubu daya da dari hudu suka tashi zuwa gasar daga Singapore da Malaysia da wasu sassa na kasar Thailand. Tsuntsayen ana sasu ne a kegin katako, wanda ake lullubewa da yadi mai kyau. Da gasar ta fara, ana daga kejin can sama […]

Dubban tsuntsaye suka shiga gasar wake-wake
Dubban tsuntsaye suka shiga gasar wake-wake

 

An fara gasar wakar tsuntsaye a kudancin Narathiwat  a kasar Thailand. Tsunsaye dubu daya da dari hudu suka tashi zuwa gasar daga Singapore da Malaysia da wasu sassa na kasar Thailand.

Tsuntsayen ana sasu ne a kegin katako, wanda ake lullubewa da yadi mai kyau. Da gasar ta fara, ana daga kejin can sama cikin iska.

Alkalan gasar na sauraren karar motsin bakin tsuntsayen su yi sharhi kan dadin murya da salo da daidaituwa da kara, a cewar Lonely Planet. Wanda ya ci gasar za a ba shi kofi da kyautar kudi.

Gasar an saba gudanar da ita kowace shekara, kuma tana cikin mafi girman gasar wakar tsuntsaye da ake gudanmarwa a kasar.

Za a rataye mutane 3 kan kisan kwamandan soji

DAGA LARABA: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Suke Buga-Buga Ko Da Suna Aikin Albashi?

UNICEF ta tallafa wa Kano da kayan adana alluran rigakafi

Ambaliya: BUA ya bai wa Maiduguri tallafin biliyan 2