Dubban ’yan Afirka masu neman zuwa Turai sun makale a Nijar
’Yan kasashen Afirka 7,000 da ke neman tsallakawa zuwa Turai sun makale a Nijar tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.
’Yan kasashen Afirka kimanin dubu bakwai da ke neman tsallakawa zuwa nahiyar Turai sun makale a Jamhuriyar Nijar tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.
Mutanen sun makale a Nijar ne sakamakon rufe iyakokin kan tudu da kuma sararin samaniya da sabuwar gwamnatin sojin kasar ta yi.
- Nijar: ’Yan ta’adda sun ƙona motocin kayan abinci a kan iyakar Burkina Faso
- Sanatan Kano ya dauki nauyin karatun dalibai 100 a fannin lafiya
Kasashen Afirka karkashen kungiyar ECOWAS da ke adawa da juyin mulkin na Nijar sun rufe iyakokinsu da ita, da zummar matsin lamba da kuma karya tattalin arzikin sojojin, wanda hakan ya hana shiga ko fitowa daga kasar.
Rashin samun damar ci gaba da tafiya ne ya sa masu neman zuwa Turai ta Nijar suka yanke shawarar komawa kasashensu, amma babu hali, saboda babu halin yin gaba ko baya.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutum 1,800 ne ke gararamba a kan tituna a Nijar, bayan cibiyoyin hukumar kula da masu gudun hijira ta duniya a kasar sun cika makil.
Yanzu kusan mutum 5,000 da ke neman komawa kasashensu ne suke zaune a cibiyoyin da hukumar take kula da su.
Mukaddashin babban jami’in hukumar a Nijar, Paola Pace, ta ce a duk wata sukan taimaka wa mutum 1,250 su koma kasashensu daga Nijar.
Amma yanzu rufe iyakokin kasar da kuma rufe sararin samaniya sun dakatar da komai tare da haddasa cunkoson jama’a a cibiyoyin.
Ta nuna damuwa cewa makalewar mutanen a kasar na iya zama dama ga masu safarar bil Adama, wadanda sun fi mayar da hankali kan masu neman zuwa kasashen Turai.
Kungiyar agaji ta COOPI ta kasar Italiya da ke da sansanin masu gudun hijira a kan iyakar Nijar da Aljeriya ta ce daga ranar 26 ga Yuli, 2023 da sojojin Nijar suka yi juyin mulki, mutum 1,300 ne suka shiga sansanin suna neman komawa kasashensu.
COOPI, wadda ke taimaka wa Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa cewa abincin da take da shi na dab da karewa, kuma babu yadda za ta samu karin abinci da magunguna sai an bude iyakar kasar.
Shugabar COOPI a Nijar, Morena Zucchelli, ta ce abincin da suke da shi a Nijar ba zai wuce karshen Agusta ba, sannan watan Satumba wa’adin kudaden da suke da shi zai cika.
“Don haka idan abubuwa ba su daidaita, an samu sauki ba, to da kyar mu ci gaba da aiki,” in ji ta.