Dubban ‘yan jam’iyyar PDP sun koma APC a Kebbi

Sama da dubu 5 ‘yan jam’iyyar PDP ne a jihar Kebbi suka koma APC. A yayin karbar masu canza shekar a hedkwatar APC da ke Birnin Kebbi Mataimakin Gwamnan jihar Alhaji Samaila Yombe wanda ya wakilci Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu shi ya jagoranci karbar ‘yan jam’iyyar. Mataimakin Gwamnan ya yaba wa sababbin ‘yan […]

Dubban ‘yan jam’iyyar PDP sun koma APC a Kebbi

Sama da dubu 5 ‘yan jam’iyyar PDP ne a jihar Kebbi suka koma APC.

A yayin karbar masu canza shekar a hedkwatar APC da ke Birnin Kebbi Mataimakin Gwamnan jihar Alhaji Samaila Yombe wanda ya wakilci Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu shi ya jagoranci karbar ‘yan jam’iyyar.

Mataimakin Gwamnan ya yaba wa sababbin ‘yan jam’iyyar APC da suka canza jam’iyya ya kuma tabbatar masu da cewa, jam’iyyar APC zata gudanar harkokinta tare da su kamar sauran tsofaffin ‘yan jam’iyyar, don ci gaba da ayyukan inganta rayuwar jama’ar jihar.