Dubban ’Yan kwana-kwana ke aikin kashe wutar dajin Kalifoniya

An baza ’yan kwana-kwana mutum dubu uku da 700 don su kashe wutar dajin Yosmite da ke Kalifoniya ta kasar Amurka. Wutar wadda ta shafe kwanaki tara tana ruruwa, ta zama ita ce irinta ta 13 a tarihin Kalifoniya, kamar yadda mahukunta suka bayyana.A wata taswira da aka baza a shafukan sadarwa, an nuna wutar […]

Dubban ’Yan kwana-kwana ke aikin kashe wutar dajin Kalifoniya
Dubban ’Yan kwana-kwana ke aikin kashe wutar dajin Kalifoniya

An baza ’yan kwana-kwana mutum dubu uku da 700 don su kashe wutar dajin Yosmite da ke Kalifoniya ta kasar Amurka. Wutar wadda ta shafe kwanaki tara tana ruruwa, ta zama ita ce irinta ta 13 a tarihin Kalifoniya, kamar yadda mahukunta suka bayyana.
A wata taswira da aka baza a shafukan sadarwa, an nuna wutar da ke ruruwa ta kusa isa wajen tara rowan da al’umma ke sha, inda akalla mutum miliyan biyu da dubu 600 da ke zaune a gabar ruwan San Francisco ke amfani da shi. Kafafen yada labarai na kasar sun ruwaito cewa nisan wutar daji daga wajen tara ruwan bai wuce kimanin mil 200 daga bangaren yamma ba. Wannan wuta ta cinye kimanin eka dubu 149 da 780 na fadin kasa, a cewar Hukumar Kwana-Kwana ta Kalifoniya, wato “Cal Fire” a sashen kula da gandun daji da kashe gobara.
Ana ta kokarin ceto al’umma daga fadawa hadarin da ke tattare da wannan wuta, domin akalla gidaje dubu hudu da 500 na fuskantar barazana. “Guguwar da ke buga na tattare da babban kalubale, domin ta kada a kudu, inda take tafiyar kilomita 421 a kowace sa’a, sannan tana tura wutar zuwa Arewa amso Gabas,” a cewar karin bayanan da aka samu.
Jaridar San Francisco Chronicle, ta ruwaito cewa ruwa na ci aba da kwarara a famfuna, kuma ba a samu matsala a ingancin ruwan ba. Kuma hukumomi a garin sun bayyana cewa, suna da wani ruwa da suka tara, ta yadda koda wutar ta haifar da matsala za a iya amfani da shi.
Sai dai akwai matsalar wutar lantarki, domin wannan birni ya dogara da wutar lantarki da ake samarwa daga madatsun ruwa, don haka aka rufe biyu daga cikin tashohin bayar da wutar lantarkin, kamar yadda wani jami’i, mai suna Jue ya bayyana wa jaridar the chronicle. Kimanin masu aikin kashe gobara dubu uku da 700, tare da talalfin kananan jiragen sama ke aiki tukuru, don shawo kan wutar.
Gwamnan Kalifoniya, Jerry Brown ya ce zai kokarin ganin ya kare jiharsa daga wannan annobar wuta, ta hanyar amfani da kudi da kayan aikin da jihar ta mallaka.