‘‘Dubbuban Katsinawa sun koma jam’iyyar APGA saboda Tata’’
Kimanin mutum dubu 400 ne suka koma jam’iyyar APGA a Jihar Katsina, a cewar Malam Sani Lawal mai Magana da yawun dan takarar Gwamnan jam’iyyar Alhaji Abdullahi Umar Tsauri, wanda aka fi sani da Tata. Mutanen sun yi sauyin shekar ne don nuna takaicinsu game da zaben fitar da gwani da aka yi a jam’iyyun […]
Kimanin mutum dubu 400 ne suka koma jam’iyyar APGA a Jihar Katsina, a cewar Malam Sani Lawal mai Magana da yawun dan takarar Gwamnan jam’iyyar Alhaji Abdullahi Umar Tsauri, wanda aka fi sani da Tata. Mutanen sun yi sauyin shekar ne don nuna takaicinsu game da zaben fitar da gwani da aka yi a jam’iyyun APC da PDP da bai yi musu dadi ba.
Malam Muhammad Salihu Lawal, ya bayyana cewa, jam’iyyarsu ta APGa ta mika wa hukumar zabe sunayen ’yan takararta, wadanda suka hada da mutum 34, wadanda za su yi takarar shiga majalisar jiha da mutum 15 da za su yi takarar ’yan majalisar wakilai, sai kuma sanatoci uku, da za su wakilci jihar a majalisar dattijai.
“Shi kuwa dan takarar gwamnanmu, Alhaji Umar Abdullahi Tsauri, wanda aka fi sani da Tata, Lawal K. Funtuwa ne zai marasa mas abaya,” inji shi.
Da Aminiya ta tuntubi Malam Muhammad Salihu kan ya nuna mata wasu daga cikin jagororin mutanen da suka sauya sheka zuwa jam’iyyarsu ta APGA, sai ya ce, ai mafi yawan wadanda suka sauya shekar ’yan PDP ne, kuma kowa yasan yadda Tata ya yi kokarin raya jam’iyyara Jihar Katsina, amma aka ki yin sahihin zaben fitar da gwani. Sannan a sauran jam’iyyun ma, akwai wadanda ba a dadada musu ba, don haka suka yanke shawarar sauyin sheka.
Malam Muhammad Salihu Lawal, ya ce nan gaba kadan za su sanar da ranar da za a yi bikin karbar wadanda suka sauya shekar.
Aminiya ta tuntubi Alhaji Lawal Abubakar Daura, wanda jigo ne a cikin kungiyar kishin Jam’iyyar APC, don jin ko yana da masaniya game da sauyin shekar mutane zuwa jam’iyyar APGA? Shi ma ya bayar da amsa da cewa, a daukacin jihar katsina akwai jam’iyyun da ba a ma sansu ba, ballantana har wani ya ce, an sauya sheka saboda takararsa.
“A Jihar Katsina talakawa ba su san jam’iyyun APGA da PDM ba, don haka shirme kawai a ce dubban mutanen sun yi sauyin sheka saboda wani dan takarar gwamna. Mu hanyar da Janar Muhammadu Buhari ya hau ita za mu bi. Don haka tun daga kansila zuwa shugaban kasa mutanen Katsina tare da APC, ba za su amince da mayaudara, ko masu nufin bata kuri’ar jama’a ba, wato ‘yan kwangila,” inji shi.