Dubun barawon akuya ta cika a Kwara
Dubun barawon ta cika ne bayan samun korafi kan yawan batan dabbobi a yankin.
Hukumar Tsaron farin Kaya ta Civil Defence (NSCDC), ta yi nasarar cafke wani wanda ake zargi da zama gawurtaccen barawon akuya a yankin Iwala na Karamar Hukumar Kaiama na Jihar Kwara.
An rawaito cewar wanda ake zargin ya shiga hannu ne yayin da yake yunkurin satar wata akuya.
- Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 11 a Kwara
- ’Yan bindiga sun yi awon gaba da daliban jami’a 4 a Nasarawa
Cafke shin ya biyo bayan korafin da mutanen yankin suka shigar kan yawan batan dabobbinsu a kauyukan Kwara ta Arewa.
Kakakin NSCDC a Jihar, Babawale Zaid Afolabi, ya tabbatar da cafke barawon a ranar Lahadi cikin wata sanarwa da ya fitar.
A cewarsa, “Tsaurara matakai da aka yi a yankin ya sa an cafke wani barawon akuya yana kokarin sace akuyar wani Hossan Abubakar,” in ji Babawale.
Ya ce tuni suka mika barawon zuwa babbar hedikwatar hukumar da ke Ilorin, sannan ana ci gaba da bincike don cafke wasu da ke aikata irin wannan dan halin.
“Bincike ya nuna cewar barawon akuyar ba mutum daya bane, suna da yawa, muna bincike don cafke ragowar,” inji kakakin.