Dubun barawon babur a lokacin sallar Juma’a ta cika
“Na fakaici jama’a ne a daidai lokacin da suka fara sallar Juma’a, na sace wannan babur da aka kama ni da shi,” inji Ibrahim Patrick, wanda ya jagoranci abokinsa mai suna Jesse James zuwa masallacin Ansar-Ud-Deen na Oluyole Ibadan, a inda asirinsu ya tonu bayan sun sace daya daga cikin baburan masallata.Wakilinmu ya ce, an […]

“Na fakaici jama’a ne a daidai lokacin da suka fara sallar Juma’a, na sace wannan babur da aka kama ni da shi,” inji Ibrahim Patrick, wanda ya jagoranci abokinsa mai suna Jesse James zuwa masallacin Ansar-Ud-Deen na Oluyole Ibadan, a inda asirinsu ya tonu bayan sun sace daya daga cikin baburan masallata.
Wakilinmu ya ce, an samu labarin bacewar babur guda biyu ne jim kadan bayan kammala sallar Juma’a, wanda a nan take daya daga cikin wadanda aka sace musu babur mai suna Kabiru Imoru, ya hanzarta sanar da jama’a da suka taimaka aka sanar da ofishin ’yan sanda na Oluyole. Majiyarmu ta ce babban jami’in ’yan sanda, DSP Sam Oke, ya dauki matakin aikewa da jami’ansa zuwa hanyoyin da ake kyautata zaton barayin za su yi amfani da su wajen tserewa da kayan da suka sace. Jami’an sun yi nasarar cafke barayin a kusa da mararrabar hanyar zuwa wannan masallaci suna tura babur din domin sun kasa kunna inji.
Da wakilinmu ya nemi jin ta bakin Patrick, ya tabbatar da cewa, “Wannan shi ne karo na farko da na taba fitowa satar babur. Na fito ne tare da abokina James kuma mun fakaici masallata ne a daidai lokacin da suka fara salla, na san cewa, hankalinsu yana can ga sallar da suke yi, ba za su waiwayi sashen da muka boye kanmu ba, sai muka lallaba muka yi awon gaba da wannan babur din.”
Dangane da babur na biyu kuma Patrick ya ce wannan babur din kadai suka sace, amma ya ambaci sunan wani jagoran barayin babur, wanda idan aka kama shi za a iya samun babur din.
Kakakin rundunar ’yan sanda ta jiha, DSP Olabisi-Okuwobi Ilobanafor ta ce wannan kame ya nuna irin matakin tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a da kwamishinan ’yan sanda Muhammed Indabawa yake dauka. Ta ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da wadanda aka kama gaban kotu.