Dubun barawon da ya addabi jama’a da satar shanu ta cika
Shugaban ’yan banga na garin Benin a Jihar Edo, Alhaji Shu’aibu Muhammed KT ya bayyana samun nasarar da kungiyarsu ta yi ta kame wani gagarumin barawon shanu da ya addabi jama’a, bayan wani artabu da suka yi da barayin tare da hadin gwiwar al’umman kauyen Ologbo, mai tazarar kilomita 25 daga garin Benin, fadar gwamnatin […]
Shugaban ’yan banga na garin Benin a Jihar Edo, Alhaji Shu’aibu Muhammed KT ya bayyana samun nasarar da kungiyarsu ta yi ta kame wani gagarumin barawon shanu da ya addabi jama’a, bayan wani artabu da suka yi da barayin tare da hadin gwiwar al’umman kauyen Ologbo, mai tazarar kilomita 25 daga garin Benin, fadar gwamnatin Jihar Edo.
Wanda ake zargin, dan asalin kasar Chadi, mai suna Muhammad Hasan, mai kimanin shekaru 25, ya shiga hannu, amma wani abokin tafiyarsa, mai suna Musa Ahmad mai shekara 22, ya tsere.
Jama’ar gari sun bayyana barayin da sauran abokan aikinsu, wadanda ba su ambata sunayensu ba, sun dade suna yi wa jama’a barazana da kuma satar shanun falake a dajin Ologbo da ke kudancin jihar ta Edo.
Alhaji Idiris Danna, daya daga cikin manyan fatomomi masu sauke bakin falaken shanu kuma babban dan kasuwa a garin Benin ya shaida wa Aminiya cewa barayin sun dade suna yi wa falake sata kuma kafin wannan babban barawon ya shiga hannu sun sace sanu ya fi a kirga.
Alhaji Shu’aibu KT ya ce, “Dubun wannan barawon ta cika ne a lokacin da aka labarta mana cewa an gansu da abokansa sun shiga yankin Ologbo. Daga nan sai ni da sauran abokan aikina muka shirya muka nufi yankin, muka samu nasara muka tarar da su cikin wannan jejin har sun kama wasu bajimai sun daure a wani sunkuru. Da suka ganmu, sai suka tasar mana haikan, muka fafata da su kuma Allah Ya ba mu nasarar kame babbansu, sauran suka arce.
Wanda ake zargin, wanda ya shiga hannu, wanda ya yi ikirarin suna sayar wa wata mata mahauciya mai suna Mama Ebo ne, shugaban ’yan bangar ya ce sun mika shi ga ’yan sandan shiyyar Opper Owa. Ita kuwa Mama Ebo, wata majiya ta ce an cafke ta a gidanta da ke Opper Owa din.
Har ya zuwa lokacin hada wannan labarin, babu karin haske daga hukumar ’yan sanda, duk da kokarin da wakilin Aminiya ya yi, amma ya ta’azzara, ’yan sandan da ke nan sun ce shugabansu D.P.O. ba ya nan, kuma ba a ba su damar yin wani bayani ba, shi kuma wayarsa a kulle take.