Dubun barayin Awaki ta cika a Gombe
An kama bata-gari masu sace-sace da fashi da makami a Gombe.
’Yan sanda sun damke wasu mutum hudu da ake zargi da satar Awaki da kuma wasu bata-gari 12 a unguwannin Malam Inna da Wuri Kesa a Jihar Gombe.
Kakakin rundunar ’yan sandan Gombe, ASP Mahid Mu’azu Abubakar ne ya sanar da hakan a madadin Kwamishinan ’Yan sandan jihar, Mista Oqua Etim.
ASP Abubakar ya bayyana cewar ababen zargin sukan yi amfani da Keke NAPEP suna shiga lunguna da sako na wasu unguwanni suna sace Awakan mutane suna sayarwa.
Ya ce dubun barayin Awakan ta cika ne yayin da jami’an ’yan sandan Gombe suka yi ram da su a maboyar su bayan rahoton sirri da suka samu kan yadda ababen zargin ke gudanar da al’amuransu.
ASP Mahid Mu’azu, ya kara da cewa suna ci gaba da gudanar da bincike kuma da zarar sun kammala za su tura su zuwa kotu.
A wani labarin mai nasaba da wannan, kakakin ’yan sandan ya kuma ce sun yi nasarar kama wasu mutum 12 da ake zargin bata-gari ne da ake zargin su da sace-sace da fashi da makami.
Mahid ya bayyana abubuwan da aka kama tate da ababen zargin da suka hada da Stabiliza 1 waya kirar Samsung Galaxy S8 plus, da wasu wayoyin salula guda 6 da bandir din atamfa 1 da adduna guda uku da wukake da sauransu.