Dubun barayin manyan wayoyin lantarki ta cika a Gombe
Sun sace manyan wayoyi da suka kai wa wasu garuruwa wutar lantarki
Dubun wasu matasa ’yan asalin Jihar Yobe ta cika bayan da suka sace wasu manyan wayoyin wutar lantarki a Jihar Gombe.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta shaida wa ’yan jarida cewa matasan masu shekaru 26 da kuma 30 ’yan asalin garin Fataskum ne a Jihar Yobe.
Da yake gabatar da su, kakakin ’yan sanda a jihar, ASP Buhari Abdullahi, ya ce a ranar 14 ga watan Yuni 2024 kamfanin samar da lantarki ba JED da ke Gombe ya kawo musu kara cewa matasa sun yi yunkuri sace manyan wayoyi sama da 100 da suka kai wa wasu garuruwa wuta.
Manyan wayoyin a cewarsa sun hada da wadanda suka kai wuta kauyen Sorodo da ke kan hanyar zuwa garin Wawa ta wuce zuwa Birin Fulani da ke Karamar Hukumar Nafada a jihar ta Gombe.
- NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa Gwamnoni Ke Rige-Rigen Yin Zaben Kananan Hukumomi?
- Ina roƙon ’yan Nijeriya da su ƙaurace wa shiga zanga-zanga — Zulum
A cewarsa, rundunar tana samun labari sashen bincikenta ya shiga aiki gadan-gadan inda suka yi nasarar kame wadannan mutane biyu da ake zargi.
Ya ce a lokacin da ake bincike, wadanda ake zargin sun amsa laifin.
ASP Abdullahi Buhari ya ce rundunar tana ci gaba da bincike kuma da zarar ta kammala za a tura matasan zuwa kotu.