Dubun mai llata da gawar matan da ya kashe ta cika
Dubun mai lalata da gawarwakin matan da ya kashe ta cika, inda rundunar ’yan sandan Jihar Ebonyi ta kama mutumin, mai suna Chukwuma, wanda ake yi wa lakabi da suna ‘Sogbodo’ sunan da ya bayyana wa ’yan sanda da ba ya so a rika kiransa da shi, ne kuma takaicin hakan ne ya buge da […]
Dubun mai lalata da gawarwakin matan da ya kashe ta cika, inda rundunar ’yan sandan Jihar Ebonyi ta kama mutumin, mai suna Chukwuma, wanda ake yi wa lakabi da suna ‘Sogbodo’ sunan da ya bayyana wa ’yan sanda da ba ya so a rika kiransa da shi, ne kuma takaicin hakan ne ya buge da aikata mugun hali, da ake zarginsa da kashe wasu mata uku, yayinda matan ke kan hanyar su ta zuwa gonakin su noma kamar yadda suka saba.
Wakilin Aminiya ya samu labarin cewa, wanda ake zargi da aikata laifin, an ce bayan ya yi kisan har jima’i yake yi da gawar duk macen da ya kashe, kamar yadda ake zarginsa da aikata wa wadannan mata uku da ake zaton shine ajalinsu.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Ebonyi, Chris Anyanwu, ya tabbatar wa Aminiya cewa wanda ake zargi da aikata laifin, ya ce “rundunar mu ce ta dana masa tarko, inda ta tura wata budurwa, ta wuce inda yake labewa yana aikata ta’asar , sai jami’an mu suka labe su ga abin da zai faru, ai kuwa ganin yarinyar ke da wuya sai Chukwuma ya fito zai aikata abin da ya saba shi ne, ’yan sanda suka cafke shi”.
Shi dai wanda ake zargi matashi ne dan shekara 20 da haihuwa, kamar yadda jami’in ’yan sandan ya tabbatar mana cewa, bayan da suka bincike shi ya shaida musu cewa “mutanen kauyen su ne suke kiransa da wani suna na shashanci, shi kuma ba ya so, su kuma sun ki su daina shi ya sanya ya yanke shawarar aikata abin da ya aikata,” in ji kakakin ’yan sandan.
Har wa yau rundunar ’yan sandan Ebonyin ta karar da cewa cikin mata uku da ya kashe a jere, a jere tau kun har kudi Naira dubu 800,500 ya sace mata. Anyanwu, wanda shi ne kakakin rundunar ’yansandan, ya ce wanda ake zargin ya yi kaurin suna wajen tare hanya yana yi wa mata kwace, ya kuma makure su, har sai sun mutu, sannan ya yi jima’i da gawar su; sai ya gudu.
Kan yadda aka gano gawar wata mace da ya kashe, jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan ya ce: “Shi ne da kansa ya amsa cewa ya yi wa wata mata mai suna Anyigor kwanton bauna a gonar ta, ya shaketa ta mutu har Lahira, sannan ya yi abin da ya so da gawar ta”. Mai laifin da ake zargi, ya bayyana wa ’yan sanda cewa kudin da ya kwace hannun wadanda ya kashe yana sayen wayoyin hannu ne da kudin, ragowar canjin kuma ya sha barasa da aka fi sani da suna kaikai.
“Da zarar an kammala bincikensa za a mika shi kotu gaban alkali don fuskantar tuhuma,” a cewar kakakin ’yan sandan.