Dubun masu damfara a ATM ta cika a Jigawa
An kama su bayan sun ciri kudi daga asusun bankin mutumin da suka damfara.
‘Yan sandan Najeriya
’Yan Sanda sun cafke wasu ’yan damfara da suka yi wa wani mutum aika-aika a injin cirar kudi (ATM) a garin Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.
An kama masu damfarar ne bayan mutumin da suka damfarar har suka kwashi kudi a asusun bankinsa ya kai kara caji ofis ranar Laraba.
- An kama katan 185 na maganin karfin maza a Kano da Jigawa
- Makarantar Dutse Model ta shirya gasar wasanni
Jami’in Hulda da Jama’a na ’Yan Sandan a Jihar Jigawa, Lawan Shisu, ya shaida wa manema labarai cewa ’yan damfarar sun saci Naira 58,000 daga cikin asusun ajiyar mutumin kafin a kama su.
Ya ce miyagun sun samu damar yi wa mutumin zamba ne bayan sun nuna masa kamar taimakon shi za su yi.
Ya ce a halin yanzu wadanda ake tuhumar na tsare a hannun ’yan sanda ana ci gaba da bincike.